Posts

Showing posts from October, 2020

An raunata wani mai gadi a ofishin jakadancin Faransa a Saudiyya

Image
An kama wani mutum a birnin Jidda na kasar Saudiyya da ake zargi da raunata wani maigadi a ofishin jakadancin Faransa da ke birnin, ta hanyar daba masa wuka. Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani a kan abin da ya haddasa harin. Sai dai harin ya biyo bayan zaman dar-dar din da ake yi a gabas-ta-tsakiya, sakamakon matsayin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya dauka na kare zanen batancin nan da aka yi na aibanta Annabi Muhammadu. Tuni dai Ofishin ofishin jakadancin Faransar ya gargadin Faransawa mazauna Saudiyya da su dinga taka-tsantsan.

Shugaban Senegal ya sallami ministocinsa 32

Image
Shugaban Senegal Macky Sall, ya rushe majalisar ministocinsa, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana. Gwamnatin tasa na da ministoci 32 da kuma sakatarori uku, kuma dukansu an sallame su. Babu wani dalili da aka bayar na sauke ministocin, ko kuma lokacin da za a naɗa wasu sabbi. A watan Maris ɗin shekarar nan ne Shugaba Sall ya lashe zaɓen shugaban ƙasar karo na biyu, sai dai 'yan adawa a ƙasar na zarginsa da daƙile wasu daga cikin manyan abokan hamayyarsa daga tsayawa takara.

YANZU-YANZU: Gwamnatin Jihar Neja Ta Hana Zagayen Mauludi

Image
 Gwamnatin Jihar Neja Ta Hana Zagayen Mauludi Biyo Bayan Rikicin Zanga-zangar Rushe SARS Gwamnatin jihar Neja ta haramta zagayen Maulidi wanda zai gudana ranar Asabar a fadin Jihar. Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne domin dakile aukuwar zanga-zangar EndSARS da ya haifar da satar kayayyakin Gwamnati da kuma fasa rumbun abinci da matasa suka yi a wasu jihohin. Daga Jamilu El Hussain Pambegua

Yan bindiga sun kai hari Masallaci a Nasarawa, sun yi awon gaba da Masallata 17

Image
Ana tsakiyan Ibada, bata gari cikin al'umma sun yi aika-aika - Masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa milyan hamsin, amma daga baya sun rage - Har yanzu ba'a samu ceto wadanda aka sace daga hannunsu ba Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari Masallaci kuma sun sace mutane 17 a unguwar Gwargwada-Sabo dake garin Gadabuke a jihar Nasarawa. An tattaro cewa wadanda aka sace sun hada da wani ma'aikacin jami'ar Ahmadu Bello Zariya, mata 3 a wasu maza 13, a cewar rahoton Daily Trust. Wani mazaunin unguwar mai suna Usman ya ce wannan abu ya faru ne daren Talata yayinda ake Sallan Isha'i. "Yan bindigan na shigowa suka fara harbin kan mai uwa da wabi, yayinda sauran suka shiga cikin Masallacin sukayi awon gaba da su cikin daji," yace. Limamin Masallacin da yaranshi kadai suka tsira.Iyalan wadanda aka sace sun samu tattaunawa da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci milyan daya-daya kan kowani mutum. "Da farko sun b

Charlie Hebdo: Turkiyya za ta shigar da ƙara kan zanen ɓatanci ga Erdogan a Faransa

Image
Turkiyya ta yi barazanar daukar mataki na shari'a da diflomasiyya kan Faransa bayan da mujallar Charlier Hebo ta wallafa zanen Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan. Zanen ya nuna shugaban ƙasar Turkiyyan yana ɗage mayafin wata mata. Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce masu shigar da ƙara sun ƙaddamar da wani bincike a hukumance kan mujallar barkwancin. Tashin hankali tsakanin Faransa da Turkiyya ya ƙaru bayan da Shugaba Emmanuel Macron ya sha alwashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki kan masu ƙarfin kishin Islama. Mista Erdogan ya yi kira ga Turkawa da su ƙaurace wa kayayakin da Faransa ke samar wa sannan ya ce Mista Mcaron na buƙatar a yi masa gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa. Lamarin ya yaɗu a sauran ƙasashen duniya, inda aka dinga ƙaurace wa kayayyaki da kuma zanga-zangar nuna adawa da Faransa da aka dinga yi a ƙasashen da Musulmai suka fi yawa da suka haɗa da Bangladesh da Kuwait da Jordan da Libiya. Shugaba Macron ya bayyana cewa an kashe malamin nan Samuel Parte ne sakamakon Musulmai na son

Gwamna Zulum ya ɗauki nauyin karatun 'ya'yan dakarun sa-kai da ke yaƙi da Boko Haram

Image
Gwamnatin Jihar Borno ta ɗauki nauyin karatun 'ya'yan mayaƙan sa-kai da aka fi sani da Civilian JTF waɗanda suka rasa rayukansu yayin yaƙi da ƙungiyar Boko Haram. Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da hakan a Maiduguri, babban birnin jihar a yau Laraba yayin wani taro da ya tara dakarun sa-kai da ke taya sojoji yaƙi da 'yan bindiga Borno. Borno BSGCopyright: BSG Kazalika gwamnan ya amince da bai wa matan waɗanda aka kashe ɗin naira 50,000 kowaccensu. Taron ya gudana ne a Jami'ar Jihar Borno. Wata sanarwa da sashen yaɗa labaran gwamnatin Borno ya fitar ta ce gwamnan ya bai wa kowane mutum ɗaya naira 20,000 na mutum 9,000 da suka halarci taron. Haka nan, an bai wa kowannensu buhun shinkafa ɗaya da kwalin taliya ɗaya da galan ɗin man girki. Yaƙin Boko Haram wanda aka shafe tsawon shekara 10 ana yi, ya yi sanadiyyar kashe mutum fiye da 36,000 sannan ya tilasta wa miliyoyi tserewa daga mahallinsu.

Masu Fafutukar Biafra sun kashe mutane ‘yan Arewa 30, sun lalata motocin bas 50, da tirela damanyan motocin ‘yan arewa – In Ji Ƙungiyar tuntuba ta Arewa.

Image
Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kuka kan zargin kashe wasu ‘yan arewa a yankin Kudancin kasarnan. Taron ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta ta nemi gwamnatocin jihohi daban-daban da su kafa kwamitocin bincike kan zargin kashe-kashen ‘yan Arewa.Sakataren yada labarai na ACF na kasa, Emmanuel Yawe a cikin wata sanarwa a Kaduna ya ce ya samu rahoto daga shugabanta na jihar a Jihar Ribas, Alhaji Ibrahim Tukur Tudunwada cewa ’yan Arewa da ke zaune a jihohin Ribas da Abia mambobin haramtattun yan asalin Biafra suna yin garkuwa da su. Ta yi zargin cewa kimanin ‘yan arewa 30 aka kashe, yayin da bas-hamsin, tirela da manyan motocin’ yan arewa a jihohin da kungiyar IPOB ta lalata. Sanarwar ta ruwaito shugaban ACF na jihar, Alhaji Tudunwada yana yabawa gwamna Wike saboda hana ayyukan kungiyar IPOB a cikin jihar. Sanarwar ta lura cewa wadanda suka tsira daga harin sun kasance cikin tsoro na har abada na barazanar rayuwarsu.ACF ta gargadi ‘yan arewa da ke shirin tafiya zuwa Ku

Batanci ga Addinin islama Musilman Nageriya sun Fara kauracewa Kayan Kasar Faransa, ku latsa koren alama domin sanin ai nihin Kayan Faransa a Nageriya

Image
Wani marubuci Mai suna datti datti ya nemi ‘yan Nageriya dadu kauracewa Anfani da Kayan kasar Faransa Daga cikin shahararrun kayayyakin da kamfanonin Kasar Faransa suke sayarwa a Nigeria akwai: (1) Total PMS (2) Total Engine oil (3) Ashaka Cement Portland da superset (Lafarge) (4) Big

Buhari ya ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba

Image
Fadar shugaban Najeriya ta ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba, sabanin yadda wasu ke zargin gwamnatocin jihohi da ƙin raba kayayyakin. Gwamnatin Najeriya ta ce tallafin da aka wawushe na wasu ƴan kasuwa ne da suka tara domin agaza wa mutane. Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa kayan abincin da mutane suka wawushe a jihohi ba na Gwamnatin Tarayya ba ne. "Na ƴan kasuwa ne da suka tara kudi don taimakawa kan wahalar da annobar korona ta jefa mutane," in ji shi. Jihohi da dama ne aka ɓalle wuraren ajiye abinci kuma aka wawushe su. Jihohin Adamawa da Kaduna da Filato da Taraba da Abuja da Cross River da Kwara da Oyo na cikin jihohin da suka fuskanci ayyukan matasan. Wasu da dama a Najeriya sun yi zargin gwamnatocin jihohi da jinkirta raba kayan agaji, wanda ya kawo wannan gaba da wasu da ake zargin ɓata-gari ne suka ɓalla wuraren ajiyar suna kwashewa. Amma wata sanarwar da jami`in yaɗa labaran ƙungiyar gwamnonin Najeriyar, Abd

Ku gaggauta rabar da duk tallafin korona da ku ka jibge a manyan shaguna - NLC ga FG, Jihohi

Image
Ku rabar da duk tallafin korona da ke jibge a manyan shaguna a fadin Najeriya - NLC ga FG, Jihohi - Fusatattun batagarin matasa sun cigaba da balle manyan shagunan ajiya na gwamnati tare da kwashe kayan abinci - A makon da ya gabata ne matasa suka fara balle wani babban shagon gwamnati a jihar Legas tare da yin awon gaba da kayan tallafin korona dake ciki - Tun bayan lokacin ake samun rahotannin balle manyan shagunan da aka ajiye kayan tallafin korona tare da kwashesu a sassan Najeriya Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi su gaggauta rabar da duk wani sauran kayan tallafin korona da ke suka jibge a manyan shagunan ajiya da ke fadin kasar nan. Kazalika, NLC ta yi Alla-wadai da barnatar da kayan tallafin korona da wasu batagari ke yi har yanzu a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da NLC ta fitar ranar Litinin mai taken, 'NLC ta bukaci a gaggauta raba duk wasu kayan tallafin korona da sauran kayan agaji'.

An sanya dokar hana fita a jihar Adamawa

Image
Gwamnatin jihar Adamawa ta sanya dokar hana fita biyo bayan lalata kaya da kuma yashe kayan abincin da ke cikin dakin ajiya na gwamnati da wasu ɓata gari suka yi. Cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sanda na jihar DSP Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar, rundunar 'yan sanda ta jihar ta shawarci mutane da su mutumta kansu su bi wannan doka, domin kare faruwar irin wannan ɓarna a jihar. Yayin da rundunar 'yan sanda ta jihar da sauran jami'an tsaro suka mutunta 'yancin al'ummar jihar, suna kuma shawartarsu da su guji aikata duk wani abu da zai iya jawo barazana ga tsaron jihar, in ji sanarwar. Haka kuma sanarwar ta ce babu yadda za a yi rundunar ta sanya idanu kan wasu ɓata gari suna aikata ɓarna ba tare da tsawatar musu ba, duk da cewa jami'anta sun yi aikinsu ta yadda ba a samu asarar rayuka ba yayin da suke hana satar da aka yi. An kuma kafa wani kwamitin hadin gwiwa na duka jami'an tsaro da za su riƙa zagaye domin tabbatar da cewa al'umma sun bi dokar k

Zakzaky na nan a raye - IMN

Image
Kungiyar Harka Islamiyya ta 'yan Shi'a a Najeriya ta ce jagoranta Sheikh Ibraheem Zakzaky na nan a raye bai mutu ba. Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta Ibrahim Musa ta ce, ya zama dole a gareta ta fito ta yi wa mutane bayanin kan jita-jitar da ake yaɗawa game da mutuwar jagoran nata. Cikin sanarwar kungiyar ta ce, ta yi imanin cewa wasu 'yan kanzagin gwamnati ne suke yaɗa wannan jita-jita domin ƙara jefa Najeriya cikin wani ruɗani. Sanarwar ta ƙara da cewa wani daga cikin iyalan Sheikh Zakzaky ya ziyarce shi a ranar Asabar 24/10/2020 a gidan yarin da ake tsare da shi a Kaduna. Kowa ya sani Sheikh na fama da rashin lafiya mai barazana ga rayuwa sakamakon raunukan da ke jikinsa, wanda wannan ba baƙon abu ba ne, in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa babu shakka wannan jita-jita ta fito ne daga gwamnati, da nufin ƙara gogawa kungiyar Harka Islamiyya ta 'yan Shi'a baƙin fenti, domin ƙara tayar da zaune tsaye. Haka kuma ta ce tunda

Babu wata Kasa da naje Ina gida Kuma haryanzu nine jagaban jihar Lagos, Tinubu

Image
Ban je ko’ina ba. Har yanzu ina rike da mukamin Asiwaju na Legas kuma har yanzu ni ne Jagaban na Legas, ”in ji Tinubu a wata hira da ya yi da su bayan ziyarar ban girma ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu. Kafafen sada zumunta sun cika da rahotanni da dama na yadda tinubu ya tashi A jirgi zuwa Paris, Faransa yayin da wata kafa ta ce yana Landan bayan abin da ya faru a ranar Talata. Tinubu ya yi Allah wadai da lamarin a Lekki a wata hira kai tsaye da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, yana mai jaddada cewa ba shi da hannu a lamarin.  Tinubu ya kuma bayyana cewa ba shi ne mamallakin kamfanin Lekki Concession Company (LCC), kamfanin da ke karbar kudin shiga a Lekki-Epe babbar hanyar karbar kudin shiga da kuma gadar hanyar Lekki-Ikoyi wadanda aka kone a sakamakon harbe-harben. A wata ziyarar da ya kai Sanwo-Olu, Tinubu ya bayyana jita-jita iri-iri a matsayin labarai na bogi. Sunce an sace ɗana.kuma Yana nan, ku ”ya kara da cewa. Tinubu wanda bai yi kasa a gwiwa ba yayin ziyarar Sanwo-

Sojojin Turkiyya na gwajin makami mai linzami duk da hanin da Amurka ta yi

Image
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tabbatar cewa sojojin kasar suna gwajin makami mai linzami samfurin S-400 da Rasha ta ƙera duk da cewa Amurka ta nuna rashin amincewarta. Kafafen yada labarai a Turkiyya sun rawaito cewa an yi gwajin farko a makon daya gabata a Lardin Sinop. Amurka dai ta yi kakkausar suka game da lamarin. Wakilin ma'aikatar tsaron Amurka ya ce irin wadannan gwaje-gwajen ba za su yi dai-dai da alƙawuran da Turkiyya ta ɗauka ba a matsayinta na ƙawar Amurka da ƙungiyar tsaro ta NATO.

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

Image
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Zamfara  Matawalle ya ce rusa rundunar SARS matsala ne ga al'ummar jiharsa  - Ya bukaci a kara tura jami'an tsaro jihar domin kawar da yan bindiga Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, a ranar Juma'a ya bayyana cewa sama da yan kasar waje 31 aka kora daga Najeriya saboda hakan ma'adinai ba bisa doka ba a jihar.  Gwamna ya kara da cewa mutane 20 yan bindiga suka kashe ranar Laraba bayan rusa rundunar SARS da gwamnatin tarayya tayi,  kisan-mutane-20-matawalle-ya-kaiwa-buhari-kuka-villa-hotuna. Gwamnat Matawalle ya bayyana hakan ne ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari inda ya bukaci a dawo masa da jami'an SARS. Ya kawo wa shugaba Buhari ziyara ne kan lamarin tsaron jihar. "Na zo ne domin bayyanawa shugaban kasa halin da jihar ke ciki.  Bayan rusa rundunar SARS mun fuskanci wasu matsaloli, musamman shekaran jiya (Laraba) inda aka kashe mutane 20 a kar

Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina

Image
Wannan satin ya kasance mai matukar tarihi a kasar Najeriya gaba daya - Masu zanga-zangar EndSARs sun zarce da kashe-kashe tare da kone-kone wanda ya koma tarzoma  - Adesina ya ce ko nan gaba Najeriya ta tarwatse, toh babu shakka kiyayya ce ta tarwatsa ta Wannan mako ne mai cike da tarihi a kasar nan. A cikin watan nan ne Najeriya ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya horemu da mu zauna lafiya tare da hada kai da kuma mantawa da tsohuwar gaba wacce ke kawo rikici. Abinda ya fara tamkar zanga -zangar lumana daga wasu matasan Najeriya a kan cin zarafin da rundunar ta musamman ta yaki da fashi da makami ke yi a Najeriya, ya koma wani abu na daban da ya kawo kashe-kashe da rikici. Tunanina da ta'aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.  -idan-najeriya-ta-tarwatse-kiyayya-ce-ta-tarwatsa-ta---femi-adesina Wasu jama'a suna alakanta hakan da kuskuren 1914 wanda aka hada yankin arewaci da kudanci har aka samu Najeriya. Tun daga nan ala

Rundunar Soji ta karbe iko da tsaron gidan gwamnatin jihar Imo

Image
Sojoji sun karbe iko da gidan gwamnatin jihar Imo - Dakarun rundunar soji sun mamaye hanyoyin shiga gidan gwamnatin jihar Imo, 'Douglas House'. - Sojojin sun yi hakane domin hana fusatattun ma su zanga-zanga samun damar shiga gidan Da sanyin safiyar ranar Laraba ne sojoji suka isa 'Douglas House' bayan dokar ta bacin da gwama ya saka ta fara aiki rundunar-soji-ta-karbe-iko-da-tsaron-gDuk da babu labarin samun wata barna yayin zanga-zangar ENDSARS a jihar Imo, wasu matasa sun yi yunkurin kona wani ofishin 'yan sanda a Ihiagwa. Da yawan mazauna jihar sun gaggauta komawa gidajensu da yammacin ranar Talata bayan sanar da baza 'yan sandan kwanton da tarzoma a fadin Najeriya. A wani labari na daban, Bata-garin matasa a ranar Laraba sun banka wa gidan iyayen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wuta. Dandazon masu zanga-zanga sun yi tururuwar fitowa domin cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da sanarwa da gwamnan jihar, Hope Uzodinma, ya fitar da yammacin ranar Tal

Da duminsa: IGP ya janye 'yan sanda masu tsaron dukkan manyan mutane a Najeriya

Image
Shugaban 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye 'yan sanda masu kare lafiya - Ya umarci janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin Najeriya a yau Laraba - Gidajen gwamnatoci, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai kadai aka amince a basu kariya Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan. Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna. Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame. "Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na gidajen gwamnati,

Sarauniya Amina: Jarumar da ta yi mulkin shekaru 34 a masarautar Zazzau

Image
Babu shakka kasar Zazzau ta taba samun wata jarumar Basarakiya da ake kira da sarauniya Amina - Ta jagooranci maza zakakurai kuma dakarun yaki har 20,000 bayan watanni da hawanta karagar mulki - Sarauniya Amina gagarumar basarakiya ce da ta kwashe shekaru 34 tana mulki kuma ta fadada arzikin masarautarta Idan har za a yi zancen mata jarumai a Najeriya, ba za a taba mantawa da sarauniya Amina ta Zazzau ba. Jarumar basarakiyar ta jagoranci rundunar yaki ta maza kuma ta kwato yankuna da yawa a kusa da kasar Zazzau. Kamar yadda rahoto ya nuna, basarakiyar an haifeta a gidan hamshakin basarake, Sarki Bakwa na Turunku a shekarar 1533 kuma a Zazzau suka rayu. Gidansu manyan masu arziki ne domin su ke siyar da tufafi, gishiri, goro, karfe da kuma dawakai. A zamanin mahaifinta, Amina tana samun horon yaki daga sojojin Zazzau, hakan ne ya gogar da ita sosai wanda daga baya ta zama shugaban mayakan. Sarauniya Amina Jarumar da ke kashe duk namijin da ya kwanta da ita. Hoto daga Tumblr. Sarki Bakwa

Kotun duniya ta bukaci a gaggauta gurfanar da Omar al-Bashir

Image
Babbar mai gabatar da kara a Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta yi kira kan tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir ya fuskanci shari'a ba tare da bata lokaci ba. Fatou Bensouda ta fada wa yan jarida a Khartoum cewa ta yi maraba da hadin kan da gwamnatin Sudan ta bayar. Ta ce kotun na fatan tura tawaga ta din-din-din zuwa Sudan din domin gudanar da bincike. An fara tuhumar Al Bashir da kisan kare dangi da laifukan yaki da kuma cin zarafin bil adama a yankin Darfur shekara 10 da ta gabata. Tun bayan hambarar da shi a shekarar da ta gabata, an same shi da laifin cin hanci da rashawa kuma yana fuskantar wasu tuhume-tuhumen.

Fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin Benin sakamakon zanga-zanga

Image
A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa wasu matasa da ke zanga-zanga sun balle gidan yari a Benin, jihar Edo - Rundunar 'yan sanda ta ce ba za ta lamunci tashin hankali ba ganin yadda aka samu gurbatattu a cikin masu zanga zangar ENDSARS - Ana zargin ma su zanga-zanga da tafka barna, su kuma ma su zanga-zanga na zargin an yi hayar batagari don su bata musu zanga-zanga Hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya (NCS) ta tabbatar da cewa fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin da ma su zanga-zanga su ka balle ranar Litinin a Benin, jihar Edo. Legit.ng Hausa ta rawaito yadda wasu batagarin matasa su ka balle wani gidan yari da ke kan titin Sapele a birnin Benin da safiyar ranar Litinin. Sakamakon hakan, gwamnatin jihar Edo ta sanar da saka dokar ta baci ta sa'a 24. A cikin wani jawabi da NCS ta fitar ranar Talata ta hannun darektan yada labarai da hulda da jama'a, Mohammed Manga, hukumar ta bayyana cewa ''ma fi yawan ma su laifin da su ka tsere

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

Image
Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara aiki kan rahoton bincike kan cin zarafin bil adama da ake zargin jami’an rundunar SARS da yi. A shekarar 1994 ne aka kafa rundunar ta SARS mai yaki da fashi da makami a fadin kasar. Sai da ‘yan kasar sun dade suna zargin jami’anta da aikata laifukan da suka hada da mugunta, cin zarafin biladama da kisa ba tare da gurfanarwa a gaban kotu ba. A hirarsu da BBC, Ministan Shari’a na Najeriyar Abubakar Malami ya ce a jiya ne hukumar kare hakkin bil adama ta kasar ta mika masa rahoton kan binciken da ta yi game da jami’an kuma tuni ya soma aiki a kansa. Game da tsawon lokacin da aka dauka kafin kwamitin ya mika rahoton nasa, Ministan ya bayyana cewa a tsarin gwamnatin kasar, idan aka gabatar mata da zargi ko koke-koke irin wadannan da ke da nasaba da cin zarafin bil adama, dole ne sai ya dauki tsawon lokaci ana bin bahasi kafin a cimma bukatar da ake da it ana binciko ainin wadanda suka aikata laifin. ‘’A karkashin Hukumar kare hakkin biladama ta kasa, mun kaf

Majalisar dattawan Najeriya ta yi zaman gaggawa na sirri kan zanga-zangar #EndSARS

Image
Majalisar dattawan Najeriya ta yi wani zaman gaggawa kuma na sirri a ɗazu inda ta cimma matsaya gabatar da wasu shawarwari ga Shugaba Muhammadu Buhari kan halin da kasar ta shiga. Kan haka ne Haruna Shehu Tangaza ya zanta da mataimakin mai tsawatawa na majalisar Sanata Alyu Sabi Abdullahi kan sakamakon zaman na dazu. Ga dai abin da ya ce da shi, sai ku latsa lasifikar ƙasa don sauraro:

MASU ZANGA-ZANGA DAGA BIRNIN LAGOS

Image
An baza jami'an ƴan sanda domin tabbatar da dokar hana fita a Legas Biyowa bayan da masu zanga-zangar sun ƙone ofishin ƴan sanda a birnin Lagos ayaudinnam.

APC: Masu zanga-zanga da sunan #EndSARS su na da boyayyar manufa

Image
- Mai Mala Buni ya yi tir da zanga-zangar #EndSARS da ake yi a Jihohi - Shugaban APC na rikon-kwarya ya ce akwai lauje a cikin nadi a tafiyar - Gwamnan Yobe ya ce za a iya samun matsala idan jama'a su ka yi sake Mukaddashin shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Mai Mala Buni, ya tsoma baki a kan zanga-zangar #EndSARS da ake ta faman yi. Mai Mala Buni ya ce zanga-zangar da ake yi ta #EndSARS a jihohin Najeriya, za ta iya kai wa ga barkewar rikici a fadin kasar nan idan aka yi sake. Gwamnan na Yobe wanda ke rike da jam’iyyar APC a matsayin shugaban rikon-kwarya ya ce akwai wata boyayyar manufa a wannan tafiya. Buni ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi dazu a gidan yada labarai na BBC Hausa a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, 2020, a shirin safe. Zanga-zangar #EndSARS wanda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane a Najeriya ta fara ne da sunan fatali da dakarun da ke yaki da masu fashi da makami. “Miyagu za su iya amfani da wannan dama su kawo hatsaniya, su rikita kasa, su t

Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja

Image
Zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS ta fara sauya salo a sassan Najeriya da ta samu karbuwa - Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa ana yawan samun kai hari a kan ma su zanga-zangar adawa da ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da alaka da kowacce zanga-zanga An fito da dakarun soji zuwa kan titunan Abuja domin shawo kan zanga-zangar ENDSARS da ta fara sauya salo. Zanga-zangar ENDSARS a Abuja ta fara sauya salo tare da neman rikidewa zuwa rikici sakamakon harin da wasu batagari ke kaiwa ma su zanga-zangar. Batagari a Abuja na kai hari kan ma su zanga-zangar nuna adawa da rundunar SARS da kuma ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS. Lamarin, a yawancin lokuta, ya haddasa gumurzu tare da zama sanadiyyar raunata mutane da kuma lalata dukiya. sauya-salon-zanga-zanga-an-sako-sojoji-zuwa-titunan-abuja. Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin ma su zanga-za

Yanzu-yanzu: An umurci dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya su koma aiki

Image
Gwamnatin tarayya ta bada umurnin dukkan ma'aikata manya da kanana su koma aiki ranar Litinin - Sanarwar ta fito ne daga bakin hukumar shugaban kasa ta yaki da annobar korona, PTF, a ranar 15 ga watan Oktoba - Amma PTF ta umurci ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin da ke karkashin FG su raba ranakun da ma'aikatan za su rika zuwa aiki don gudun cinkoso Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba. Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata. Ma'aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da waɗanda ke yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki. Amma PTF ta umurci ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin da ke karkashin FG su raba ranakun da ma'aikatan za su rika zuwa aiki don gudun cinkoso Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan

Ku daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen maganin ciwon idanu'

Image
Dr. Ibrahim Yuguda, ya gargadi 'yan Nigeria da su daina amfani da fitsari, gishiri, sukari ko ruwa da kashin shanu wajen magance ciwon idanu - Likitan ya gargadi masu sayen maganin ciwon idanu ba tare da izinin likitoci ba, yana mai cewa yin hakan zai kara dagula lissafi ne ba wai kawo waraka ba - A cewar Dr. Ibrahim, zuwa gwaji asibiti shine kadai mafita ta sanin lalurar idanun, da kuma yadda za a shawo kan matsalar da ta ke damun su Wani kwararren likitan idanu a asibitin koyarwa na Aminu Kano, Dr. Ibrahim Yuguda, ya gargadi 'yan Nigeria da su daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen magance ciwon idanu. Da ya ke zantawa da manema labarai a bukin 'ranar gani' ta duniya a Kano, Yuguda ya ce babban kuskure ne amfani da sukari, gishiri, ruwa, fitsari ko kashin shanu don maganin ciwon idanu. Ya bayar da shawarar cewa, zuwa gwaji asibiti shine kadai mafita ta sanin lalurar idanun, da kuma yadda za a shawo kan matsalar da ta ke damun su. 

Gwamnan Ribas ya shiga cikin masu zanga-zanga bayan ya haramta #EndSARS

Image
Nyesom Wike ya shiga cikin masu zanga-zangar #EndSARS a Fatakwal - Gwamnan ya lashe aman da ya yi na cewa ba zai bari ayi zanga-zanga ba - Wike ya ce dama tun farko ya na cikin wadanda su ke adawa da F-SARS A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, 2020, gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya lashe amansa na haramta zanga-zangar da ake yin a #EndSARS. Mai girma Nyesom Wike ya shiga cikin sahun masu wannan zanga-zanga, har kuma ya yi kira da a yi wa hukumar ‘yan sandan Najeriya garambawul. Gwamnan ya yi wannan ne bayan kwana guda da fitar da jawabi inda ya ce ba zai yarda da zanga-zanga a jiharsa ba, ganin cewa IGP ya rusa SARS. Da ya ke jawabi a gaban masu zanga-zangar, Wike ya ce ko da ya ke ba goyon bayan abin da jama’an su ke yi, ya na cikin masu sukar aikin ‘yan sanda. Gwamna Wike ya ce babu gwamnan da ya kalubalanci jami’ar tsaro kamar yadda ya yi a baya. “Ba na goyon bayan mu zo nan. Na rantse zan kare lafiya da dukiyoyin mutanen jihar Ribas. Jinanan jihar Ribas ya na da daraja a wurina.

Kasafin Kudi Na 2021: Gwamnatin Tarayya Zata Ciyo Bashin Biliyan 709.69 Domin Aiwatar Da Kasafin – Ministan Kudi

Image
Gwamnati na son cin bashin kimanin Naira biliyan 709.69 daga kungiyoyin masu ruwa da tsaki da na bangarorin biyu. Gwamnatin Najeriya za ta ciyo bashi daga kafofin cikin gida da na kasashen waje, gami da kungiyoyin hada-hadar kudi da na bangarorin biyu, don daukar nauyin gibin kasafin kudin tarayya na 2021. Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed, ce ta fadi haka a ranar Talata a yayin gabatar da bayanan kasafin kudin a Abuja. A cewar Ministan, rancen daga hanyoyin samun kudaden shiga na cikin gida da na kasashen waje an tsara zai bayar da kusan Naira tiriliyan 2.14 kowannensu, yayin da rancen daga bangarori da dama da na bangarorin biyu za su samar da kimanin Naira biliyan 709.69 da kuma cinikayyar cinikayya ta kai kimanin biliyan 205.15. Misis Ahmed ta ce, sauran hanyoyin samar da gibin daga cinikayyar da aka yi ne na kamfanonin gwamnati. Kasafin kudin farfado da tattalin arziki da juriya Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da “Kasafin kudin shekarar 2021

SARS a Najeriya : Majalisar wakilai na son a riƙa biyan mutanen da jami'an SARS suka ci zarafi diyya

Image
Shugaban majalisar wakilan Najeriya ya buƙaci babban sufeton 'yan sandan ƙasar ya ɓullo da wata hanya ta gano duk wani ɗan Najeriya da 'yan sanda suka azabtar don tabbatar da biyansu diyya. Femi Gbajabiamila, ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da hukumomi ke yi don kawo ƙarshen zanga-zangar nuna adawa da zaluncin 'yan sanda a Nijeriya. Duk da rushe sashen 'yan sandan SARS da ya yi ƙaurin suna, masu zanga-zangar sun ci gaba da jerin gwano har a jiya Talata, lokacin da aka sanar da kafa sabuwar rundunar SWAT don maye gurbin SARS. Biyan fansa ga wadanda suka mutu ko suka tagayyara sakamakon azabtarwar 'yan sandan, na daga cikin bukatun masu zanga-zangar neman kawo karshen cin zarafin jama'a da ake zargin 'yan sandan da yi. A cewar kakakin, majalisar ta cimma matsayar sanyaya rayukan iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hannun 'yan sandan kasar ta hanyar biyansu diyya. Femi Gbajabiamila, ya ce majalisar zata karbi jerin sunayen mutanen tare da yin tana

EndSARS: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS

Image
Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta ce ta kwace makaman da ke hannun jami'an sashen dakile fashi da makami FSARS na jihar - Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu ya bayyana hakan, yana mai cewa, yanzu an rushe sashen jami'an, ba sa kara yin aiki - Haka zalika, ya karyata rahotannin cewa an kashe wami mai zanga zanga a Surulere a ranar Litinin, yana nuni da cewa, dan kallo ne aka kashe Kwamishinan 'yan sandan jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya ce bi umurnin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, na ruguza sashen rundunar SARS. Odumosu, wanda ya gana da wasu lauyoyi da suke zanga zanga kan cin zarafin da jami'an SARS ke yiwa jama'a, ya ce tuni aka kwace makamai daga hannun jami'an rundunar SARS Odumosu, wanda ya jinjinawa masu zanga zangar bisa jagorancin lauyan kare hakkin bil Adama, Inibehe Effiong, na nuna dattako, ya kuma ce babu mutum daya da aka kashe a zanga zangar jihar.

Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban Kasuwa Har Lahira.

Image
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu kisan gilla ne sun harbe shugaban kasuwar Harbour dake karamar hukumar Udu ta jihar Delta, Misis Freedom Odiete har lahira. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, kuma wannan shine karo na uku da maharan ke neman rayuwarsa.Mista Freedom dai wanda aka fi sani da Opito an yi masa kwanton bauna ne a yankin Ekete daidai mahadar babbar hanyar DSC a karamar hukumar. A ‘yan bindigar suka yi masa dirar mikiya. Daga nan ne suka harbe shi a kafadarsa ta dama inda ya yi karfin hali ya tsere amma suka sake bin shi har wurin da ya sami mafaka a kan hanyar Orhuwhorun suka ci gaba da harbinsa ba tare da kakkautawa ba. ba zai rasa nasaba da wata cacar-bakin da ake yi tsakanin matasan yankin Ovwian da na Owhase kan mallakar wasu kasuwar.

Sama da mutum miliyan tara na buƙatar agajin gaggawa a Sudan – MDD

Image
Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan tara a Sudan na buƙatar agajin gaggawa sakamakon mummunar ambaliya. Wannan adadiin na nufin kusan kashi ɗaya cikin huɗu na yawan al’ummar ƙasar ke cikin wani hali. A wata hira da BBC, jami’in hukumar a Khartoum (Babagana Ahmadu), ya ce ambaliyar ta yi ɓarna sosai ga fannin noma inda ya ce ta lalata gonaki hecta miliyan uku da sama da miliyan na ton ɗin hatsi. A watannin da suka gabata, sama da mutane ɗari suka mutu sakamakon ambaliyar wacce kuma ta lalata amfanin gonar da ake nomawa don fitarwa ƙasashen waje. Sudan kuma na fuskantar matsalar tattalin arziƙi tare da ƙarancin man fetur.

Yan bindiga sun kashe wani basarake a Kaduna

Image
Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe Mai Garin Runji Alhaji Musa Abubakar. Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun afka gidansa ne da sanyin safiyar Lahadi a garin na Runji da ke Ƙaramar Hukumar Ikara ta Jihar Kaduna. Jaridar ta ruwaito cewa ɗan mai garin, Suleiman Musa wanda shi ma mai gari ne a ƙauyen Rafin Rogo, shi ya tabbatar musu da wannan labari. Haka zalika Kantoman Ƙaramar Hukumar Ikara, Salisu Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kai jami'an tsaro ƙauyen na Runji tare da tabbatar da cewa za a gano waɗanda suke da hannu a kisan mai garin kuma a hukunta su. Article share tools

Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki

Image
Karfin hali ya kai wani matashi mai suna Kabiru shiga majalisar dokoki sata - Bai sani ba ashe na'urar CCTV na daukansa yayinda yake satan - Tuni an damke shi kuma an sanar da jami'an tsaron majalisar dokokin dake Abuja Wani matashi mai suna Kabiru a ranar Juma'a ya fasa cikin majalisar dokokin tarayya inda ya shiga ofishin wani dan majalisar wakilai ya kwashe daloli da wasu kayayyaki. Wannan abu ya faru misalin karfe 2:30 na rana inda matashin yayi amfani wani mukulli na daban. An yi zargin Kabiru da kwashe daloli da kayayykin ofis irinsu na'urar kwamfuta, na'urar fotocofi da printer.SaharaReporters ta tattaro cewa Kabiru ya kasance hadimi ga wani dan majalisa daga Adamawa kuma sannanen mutum ne a majalisar. Jami'an tsaron majalisar sun gane fuskarsa a bidiyon na'urar CCTV da ta daukeshi yana fashin. A yayinda ake tattara wannan rahoton, wasu yan majalisa wanda ya hada da mai magana da yawun mambobin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, na wajen da aka kama ma

Fadar Shugaban Kasa Za Ta Lakume Biliyan 49…

Image
Fadar Shugaban Kasa Za Ta Lakume Biliyan 49 a kasafin kudin 2021… Kasafin kudin na 2021 ya nuna cewa fadar shugaban kasa za ta kashe 49,058,552,834 a kan kashe-kashe na yau da kullun, wanda ya kunshi yawanci na albashi da kari, sayen kayayyaki da aiyuka da kuma amfani da sauransu. Ma’aikatar tsaro itama za ta lakume N840,559,082,105 a kan wannan kwatankwacin kudaden, yayin da na Ma’aikatar Harkokin Waje ya kai N75,598,309,134. Sauran sune; Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu, 53,041,805,719; Ma’aikatar Cikin Gida, N227,015,559,081; Ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya, N7,820,057,428; Odita-Janar na Tarayya, N4,420,905,177; Ma’aikatar harkokin ‘yan sanda, N441,392,646,603; Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki, N21,806,808,263; Ofishin mai ba da shawara kan tsaro (NSA), N134,095,146; 653; Hukumar Kula da Ba da Tallafin Kayayyakin Kayayyaki (ICRC) N1,189,334,898, da sauransu. Kudaden da aka kasafta don kashe kudade na yau da kullun a bangaren zartarwa na gwamnati a shekarar 2021 ya kai

Turka-turka: Kasafin Kudin Shekarar 2021 Da Buhari Ya Gabatar Jiya Ya Sabawa Dokar Najeriya, In Ji Atiku Abubakar…

Image
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce kudirin kasafin kudi na 2021 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a gaban Majalisar Tarayya a ranar Alhamis ya saba wa Dokar Kasafin Kudin 2007. A wata sanarwa da Atiku ya fitar ya bayyana cewa sashi na II, sashi na 12 (1) na dokar ya bayyana cewa jimlar kashe kudade da kuma jimillar kudin da majalisar kasa ta ware a kowace shekara ta kudi ba za su wuce yawan kudaden da aka kiyasta tare da gibi ba. Ya kuma kara da cewa dokar ta ce abin da aka kashe ba zai wuce kashi uku cikin 100 na yawan kudin da ake samu a cikin gida (GDP) ba. Atiku ya lura cewa gibin kasafin kudi a cikin kudirin shine is 5.21 tiriliyan, wanda ya ce ya kai sama da kashi 3.5 na GDP na 2019 na Najeriya. “Wannan ya sabawa dokar kasafin kudi na 2007,” in ji shi. A cewarsa, Najeriya na da GDP kimanin dala biliyan 447 a shekarar 2019. “Kashi uku cikin 100 na wannan kudin sun kai dala 13. Biliyan 3, wanda a halin yanzu na canjin kuɗin ₦ 379 zuwa $ 1, ya ba ka ad

Ƴan Najeriya miliyan 79 ke cikin matsanancin talauci a 2018 - Bankin Duniya

Image
Wani sabon rahotan Bankin Duniya ya ce Najeriya ce ƙasa mafi yawan matalauta a ƙasashen kudu da hamadar sahara, wanda ƴan ƙasar miliyan 79 a 2018 ke cikin matsanancin talauci. Najeriya ke da kashi 20 cikin 100 na matalauta a yankin, kamar yadda rahotan bankin kan talauci ya nuna. Sannan rahoton ya kara da cewa annobar korona za ta sake tursasa wa mutum miliyan 40 shiga matsanancin ƙangin talauci a kudu da hamadar sahara. Ya ce, "Kusan rabin mutanen da ke cikin talauci a kudu da hamadar saharar Afirka na rayuwa ne a ƙasashe biyar da suka hada da Najeriya da DR Congo da Tanzania da Ethiopia sai kuma Madagascar. "A Najeriya, yankunan arewaci talaucin ya fi kamari, yayinda a yankunan kudu da garuruwan bakin ruwa abin da dan sauki." Bankin duniya ya ƙiyasta cewa annobar Covid-19 za ta sake jefa karin mutum miliyan 88 zuwa 115 cikin matsanancin talauci a wannan shekarar, adadin da ya ƙiyasta zai karu zuwa miliyan 150 a 2021, ko da yake ya danganta na yanayin tattalin arzikin ƙ

Fashewar bututun iskar gas a Lagos ya jawo gobara

Image
Gobara ta tashi a wata tashar iskar gas da ke yankin Baruwa a jihar Legas da ke kudu maso yammaicn Najeriya. Wutar ta tashi ne da misalin ƙarfe 6 na asuba a cewar hukumomi amma ba su bayar da wasu ƙarin bayanai kan lamarin ba. Wasu mazauna yankin sun fara wallafa bidiyo da hotunan abin da ya faru a shafukan sada zumunta.

Abin da ake sa ran Buhari zai gabatar wa majalisa na kasafin kuɗin 2021

Image
ASALIN HOTON, PRESIDENCY A ranar Alhamis ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2021 gaban Majalisar Tarayyar ƙasar. Sai dai kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Barau Jibril ya bayyana, gabatar da kasafin kuɗin na wannan shekarar zai sha bamban da na sauran shekaru sakamakon annobar cutar korona. A cewarsa, za a bi ƙa'idojin kare yaɗuwar cutar da kuma yin tanadi ta yadda ba za a samu cunkoso ba yayin gabatar da kasafin kuɗin, hakazalika ba za a daɗe wurin gabatar da kasafin kudin ba kamar yadda ake yi ba a da. An dai ɗora ƙudurin kasafin kuɗin na 2021 kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 379 da kuma mizanin gangar man fetur guda a kan dala 40, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 1.86 a kullum. A bara dai an amince da kasafin kudin ne kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 305, haka kuma an saka mizanin gangar man fetur guda a kan dala 57, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 2.18 a kullum