Kotun duniya ta bukaci a gaggauta gurfanar da Omar al-Bashir



Babbar mai gabatar da kara a Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta yi kira kan tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir ya fuskanci shari'a ba tare da bata lokaci ba.

Fatou Bensouda ta fada wa yan jarida a Khartoum cewa ta yi maraba da hadin kan da gwamnatin Sudan ta bayar.

Ta ce kotun na fatan tura tawaga ta din-din-din zuwa Sudan din domin gudanar da bincike.

An fara tuhumar Al Bashir da kisan kare dangi da laifukan yaki da kuma cin zarafin bil adama a yankin Darfur shekara 10 da ta gabata.

Tun bayan hambarar da shi a shekarar da ta gabata, an same shi da laifin cin hanci da rashawa kuma yana fuskantar wasu tuhume-tuhumen.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)