HANYAR DA ZA’A BI DOMIN A INGANTA TSARON CIKIN GIDA NIGERIA

HANYAR DA ZA’A BI DOMIN A INGANTA
TSARON CIKIN GIDA NIGERIA
Daga Alkalamin Malam Datti Assalafiy

A cikin kowace kasa a duniya, ‘yan sanda sune suke da alhakkin tabbatar da tsaro na cikin gida, idan bukata ta kama suna taba
aikin soja, babu Kasar da ta zauna lafiya face sai da ta gyara ‘yan sandan ta 

Amma a Kasarmu Nigeria me yasa aka dakatar da diban sabbin ‘yan sanda masu mukamin Constable?
Yanzu muna cikin shekara na biyu da aka dakatar da diban sabbin ‘yan sandan Nigeria masu mukamin Constable, sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin Maigirma tsohon shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria IGP
Muhammad Abubakar Adamu (rtd), da kuma shugaban hukumar kula da aikin ‘yan sanda na kasa (Chairman Police Service
Commission) akan batun diban sabbin ‘yan sanda masu mukamin Constable Maigirma tsohon shugaban ‘yan sanda IGP Muhammad Abubakar Adamu yace shi yake da ikon diban sabbin kuratan ‘yan sanda bisa dokar aikin ‘yan sanda, Chairman Police
Service Commission sunce su ke da ikon diban kuratan, don haka sai rashin jituwa ya shiga tsakani Tsohon IGP Muhammad Abubakar Adamu bai tsaya sa’insa da Chairman Police Service Commission ba, ya fara shirin diban sabbin ‘yan sanda, har ma anyi screening da medical
checkup, saura a rubuta exam, ana cikin haka sai Police Service Commission suka maka
tsohon IGP a kotu, sai kotu ta dakatar da shirin diban sabbin kuratan ‘yan sandan, har zuwa yau ba’a sasanta ba

A halin da Nigeria take ciki yanzu, kowani wata sai an samu adadi mai yawa na ‘yan sanda da suke ritaya daga aikiwasu na mutuwa a bakin aiki, babu wani tsari na cike
gurabansu, wato kullun rundinar ‘yan sandan 

Nigeria da take dauke da alhakkin tabbatar da tsaron cikin gida Nigeria tana kara samun
rashin yawan jami’anta wanda ya kamata ace ta maye gurbinsu da sabbin ‘yan sanda 

Babu wanda yake da masaniya akan sai yaushe kotu zata zartar da hukunci domin a cigaba da diban sabbin ‘yan sanda, amma
magana ta gaskiya wannan sabani da aka samu yana matukar illata tsaron cikin gida

Nigeria, kuma akwai bukatar Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ya saka baki akan wannan
matsala Idan muka dubi tarihi, turawan mulkin mallaka sun kafa rundinar ‘yan sandan Nigeria a Lagos wajen shekaru 150 da suka
wuce, har zuwa lokacin da Nigeria ta samu ‘yan cin kai babu hukumar kula da aikin ‘yan sanda Police Service Commission (PSC),
hukumar PSC bata wuce shekaru 40 da kafuwa ba, idan an fahimci wannan, tun daga lokacin da aka kafa rundinar ‘yan sanda, ofishin Maigirma shugaban ‘yan sanda IGP ke diban sabbin ‘yan sanda masu mukamin ASP Constable PC
Bayan an kafa Police Service Commission sai ya zama su ke da alhakkin kula da diban ‘yan
sanda masu mukamin ASP, amma mukamin Constable PC har zuwa shekarar 2015 ofishin IGP ke gudanar wa, to amma me yasa yanzu PSC ke neman kwace wa daga ofishin IGP?

Nayi bincike mai zurfi akan wannan, magana ne na cewa yanzu aikin ‘yan sanda ya gyaru
a Gwamnatin Baba Buhari Maigaskiya, mutane da kudinsu suna neman shiga aikin
basa samu, wasu suna fadawa hannun ‘yan damfara a karbe kudaden su, kuma basu
samu ba, anan ne interest ya shigo har aka samu wannan sabanin
Batun diban ASP Cadet da kuma sabunta makarantar ‘yan sanda na Wudil dake jihar Kano zuwa Police Academy (POLAC) ta dawo
irin makarantar sojoji Defence Acedamy, ni Datti Assalafiy inda zan samu damar ganin Maigirma shugaban kasa, zan bashi shawara
cewa ya canza tsarin POLAC, a mayar dashi duk bayan shekara 7 ko 10 kafin a debi sabbin ASP, idan hakan ba zai yiwu ba to a
rage yawan wadanda ake diba a makarantar POLAC da kaso 85 cikin 100 su dawo kaso 15
kadai ya wadatr Abinda yake faruwa shine, kudin da
Gwamnatin Nigeria take kashewa wajen kulawa da daliban POLAC da yadda ake dibansu da yawa ya isa ayi amfani da kudin
wajen diban sabbin Constable dubu 50 duk shekara Dalilin fadin wannan maganar shine: daga
kan Inspector zuwa karamin matsayi na Constable, sune aikin ‘dan sanda, su ke daukar bindiga, su ke bada tsaro, su ke bincike da kama mai laifi, amma sai ya
zamana ba’a damu da dibansu ba, anfi damuwa da diban wadanda aikinsu shine su

bada umarni kawai, abinda ASP 100 zasu yi ASP 1 zai iya, saboda aikin ‘dan sanda Discipline ne da kuma Order d  Directive Yaran da ake diba a POLAC yaran manya ne
da ‘yan siyasa, yawanci ba kishi garesu ba, suna fitowa a matsayin ASP bukatarsu ina inda kudi yake? (a fahimci ne ba dukansu ba)
Sannan ASP zuwa sama sai dai ya bada umarni, don haka babu bukatarsu da yawa, indai kishin Nigeria da kuma gyara ake so a
harkan tsaron cikin gida to ya kamata Gwamnati ta mayar da hankali wajen diban kananan ‘yann sanda, ya zama suna da yawa, tunda sune ke aiki
ASP da ake diba yanzu sunyi yawa, kuma saboda yawan da sukayi sun rasa ma inda zasuyi aiki, wasun su sun dawo suna aikin kananan ‘yan sanda, kamar aikin Charge
Room Officer (CRO) da Beat da Patrol, wanda hakan yana matukar zubar da darajan aikin ‘yan sanda Sannan a duba a gani, yawan ‘yan sandan

Nigeria ba su kai dubu dari biyar ba, idan aka raba ‘yan sandan domin su bada kariya wa shugabannin siyasa, tun daga kan shugaban kasa har zuwa kan Chairman da Sarakunan gargaji, da wadanda ake turawa suna tsaron
bankuna da kamfanoni da kayan Gwamnati masu muhimmanci, da manyan attajirai, da Diplomats, sai a ga adadin ‘yan sanda da suka
rage bai kai dubu dari ba wadanda zasu bada tsaro wa ‘yan Nigeria Miliyan 200,Don haka ta kowace fuska akwai bukatar
Gwamnatin Nigeria ta dage wajen diban sabbin ‘yan sanda musamman masu mukamin
Constable, ya zama ace yawa ‘yan sandan  Nigeria ya kai Miliyan 1, sannan a gyara harkan bada horo na ‘yan sanda, a basu kayan aiki na zamani, Insha Allahu Internal
security zai inganta a Nigeria
Muna fatan Allah Ya tabbatar mana da tsaro da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria Amin


Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)