Buhari ya ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba



Fadar shugaban Najeriya ta ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba, sabanin yadda wasu ke zargin gwamnatocin jihohi da ƙin raba kayayyakin.

Gwamnatin Najeriya ta ce tallafin da aka wawushe na wasu ƴan kasuwa ne da suka tara domin agaza wa mutane.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa kayan abincin da mutane suka wawushe a jihohi ba na Gwamnatin Tarayya ba ne.
"Na ƴan kasuwa ne da suka tara kudi don taimakawa kan wahalar da annobar korona ta jefa mutane," in ji shi.

Jihohi da dama ne aka ɓalle wuraren ajiye abinci kuma aka wawushe su.

Jihohin Adamawa da Kaduna da Filato da Taraba da Abuja da Cross River da Kwara da Oyo na cikin jihohin da suka fuskanci ayyukan matasan.

Wasu da dama a Najeriya sun yi zargin gwamnatocin jihohi da jinkirta raba kayan agaji, wanda ya kawo wannan gaba da wasu da ake zargin ɓata-gari ne suka ɓalla wuraren ajiyar suna kwashewa.

Amma wata sanarwar da jami`in yaɗa labaran ƙungiyar gwamnonin Najeriyar, Abdurrazak Barkindo ya fitar, ta ce gwamnonin ba sa ƙwange ko boye kayan agajin, suna rabar da abin da ya shiga hannunsu ga mabukata, face wanda suke ajiye wa don ko-ta-kwana.

"Kayan da ake magana an gani ana wawashewa a wasu jihohin na wani gangamin `yan kasuwa ne da ke taimakawa mutane," a cewar sanarwar ƙungiyar gwamnonin.

Haka nan, Malam Garba Shehu ya ce ƴan kasuwa ne suka tara kudi kuma suka samu masana'antu suna yi masu kayayyaki na musamman.
Ya ƙara da cewa kamar yadda gwamnati take da nata tsarin tallafawa al'umma haka ƴan kasuwa suna da nasu tsarin.

Duk da cewa Gwamnatin Tarayyar na alakanta kayan agajin da gangamin ƴan kasuwa, amma ba ta fito fili ta ce ta kammala raba nata kayan da ta yi alkawarin tallafa wa gajiyayyu ba.

Ko da yake mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya ce ita gwamnati ba ta rabuwa da tanadin kayan abinci a kodayaushe, saboda da shi take amfani wajen taimaka wa al`ummomin da masifa ta auka musu.

Shugaba Buhari dai ya nuna rashin jin dadinsa dangane da wawason da wasu `yan kasar suka yi a wuraren ajiyar na gwamnati da ma wasu kantuna da gidajen wasu `yan siyasa.

Ya bayyana halayyar da cewa ta saɓa da shaidar da aka yi wa al`umar kasar ta nagarta.Buhari ya ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba Yayin da gwamnatin Najeriyar ke yin tir da dabi`ar masu kwasar ganimar, wasu masu sharhi kuma a kan al'amura na cewa wawason manuniya ce game da halin kunci da matsi, da masu karamin karfi suka samu kansu, wanda ke bukatar mahukunta su hanzarta wajen daukar matakin yassare musu.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)