Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Zamfara
Matawalle ya ce rusa rundunar SARS matsala ne ga al'ummar jiharsa
- Ya bukaci a kara tura jami'an tsaro jihar domin kawar da yan bindiga Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, a ranar Juma'a ya bayyana cewa sama da yan kasar waje 31 aka kora daga Najeriya saboda hakan ma'adinai ba bisa doka ba a jihar.
Gwamna ya kara da cewa mutane 20 yan bindiga suka kashe ranar Laraba bayan rusa rundunar SARS da gwamnatin tarayya tayi, kisan-mutane-20-matawalle-ya-kaiwa-buhari-kuka-villa-hotuna.
Gwamnat Matawalle ya bayyana hakan ne ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari inda ya bukaci a dawo masa da jami'an SARS. Ya kawo wa shugaba Buhari ziyara ne kan lamarin tsaron jihar. "Na zo ne domin bayyanawa shugaban kasa halin da jihar ke ciki.
Bayan rusa rundunar SARS mun fuskanci wasu matsaloli, musamman shekaran jiya (Laraba) inda aka kashe mutane 20 a karamar hukumar Talata Mafara, " Matwalle yace
"Saboda haka na bukaci shugaban kasa ya kawo dauki don ganin yadda za'a tura jami'an tsaro kare mana jihar."
kisan-mutane-20-matawalle-ya-kaiwa-buhari-kuka-villa-hotuna.html
Comments
Post a Comment