Yan bindiga sun kai hari Masallaci a Nasarawa, sun yi awon gaba da Masallata 17



Ana tsakiyan Ibada, bata gari cikin al'umma sun yi aika-aika
- Masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa milyan
hamsin, amma daga baya sun rage
- Har yanzu ba'a samu ceto wadanda aka sace daga
hannunsu ba
Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da
mutane ne sun kai hari Masallaci kuma sun sace mutane 17 a
unguwar Gwargwada-Sabo dake garin Gadabuke a jihar
Nasarawa.
An tattaro cewa wadanda aka sace sun hada da wani
ma'aikacin jami'ar Ahmadu Bello Zariya, mata 3 a wasu maza
13, a cewar rahoton Daily Trust.
Wani mazaunin unguwar mai suna Usman ya ce wannan abu
ya faru ne daren Talata yayinda ake Sallan Isha'i.
"Yan bindigan na shigowa suka fara harbin kan mai uwa da
wabi, yayinda sauran suka shiga cikin Masallacin sukayi awon
gaba da su cikin daji," yace.
Limamin Masallacin da yaranshi kadai suka tsira.Iyalan wadanda aka sace sun samu tattaunawa da masu
garkuwa da mutanen kuma sun bukaci milyan daya-daya kan
kowani mutum.
"Da farko sun bukaci milyan 50, amma da muka cigaba da
tattaunawa da su, sai suka ce mu biya milyan kan kowani
mutum," ya kara.
Duk yunkurin ji daga bakin kakakin yan sandan jihar Nasarawa,
ASP Rahman Nansel, ya ci tura.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)