Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina



Wannan satin ya kasance mai matukar tarihi a kasar Najeriya gaba daya - Masu zanga-zangar EndSARs sun zarce da kashe-kashe tare da kone-kone wanda ya koma tarzoma

 - Adesina ya ce ko nan gaba Najeriya ta tarwatse, toh babu shakka kiyayya ce ta tarwatsa ta Wannan mako ne mai cike da tarihi a kasar nan. A cikin watan nan ne Najeriya ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya horemu da mu zauna lafiya tare da hada kai da kuma mantawa da tsohuwar gaba wacce ke kawo rikici. Abinda ya fara tamkar zanga

-zangar lumana daga wasu matasan Najeriya a kan cin zarafin da rundunar ta musamman ta yaki da fashi da makami ke yi a Najeriya, ya koma wani abu na daban da ya kawo kashe-kashe da rikici. Tunanina da ta'aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. 

-idan-najeriya-ta-tarwatse-kiyayya-ce-ta-tarwatsa-ta---femi-adesina

Wasu jama'a suna alakanta hakan da kuskuren 1914 wanda aka hada yankin arewaci da kudanci har aka samu Najeriya. Tun daga nan alakar ta kasa zama guda daya tsakanin yankunan. Wutar kiyayya ta cigaba da ruruwa. Idan har Najeriya ta tarwatse, ko yanzu ko a nan gaba, babu shakka kiyayya ce ta kawo hakan. 

Ta yaya jama'a za su cigaba da daukar gaba suna amfani da ita wurin kashe junansu, tarwatsa shugabanci da kuma hana zaman lafiya? 

"Idan muka rasa wa za mu ki, sai mu fara kin kanmu," wani marubuci yace. 

-idan-najeriya-ta-tarwatse-kiyayya-ce-ta-tarwatsa-ta---femi-adesina.html

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau