SARS a Najeriya : Majalisar wakilai na son a riƙa biyan mutanen da jami'an SARS suka ci zarafi diyya



Shugaban majalisar wakilan Najeriya ya buƙaci babban sufeton 'yan sandan ƙasar ya ɓullo da wata hanya ta gano duk wani ɗan Najeriya da 'yan sanda suka azabtar don tabbatar da biyansu diyya.

Femi Gbajabiamila, ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da hukumomi ke yi don kawo ƙarshen zanga-zangar nuna adawa da zaluncin 'yan sanda a Nijeriya.

Duk da rushe sashen 'yan sandan SARS da ya yi ƙaurin suna, masu zanga-zangar sun ci gaba da jerin gwano har a jiya Talata, lokacin da aka sanar da kafa sabuwar rundunar SWAT don maye gurbin SARS.

Biyan fansa ga wadanda suka mutu ko suka tagayyara sakamakon azabtarwar 'yan sandan, na daga cikin bukatun masu zanga-zangar neman kawo karshen cin zarafin jama'a da ake zargin 'yan sandan da yi.

A cewar kakakin, majalisar ta cimma matsayar sanyaya rayukan iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hannun 'yan sandan kasar ta hanyar biyansu diyya.
Femi Gbajabiamila, ya ce majalisar zata karbi jerin sunayen mutanen tare da yin tanadin biyan iyalansu diyyar a cikin kasafin kudin shekarar 2021.Honourable Ahmad Sarkin Fulani, dan majalisar wakilai ne daga jihar Zamfara ya kuma shaida wa BBC cewa, dukkan wasu bayanai na wadanda 'yan sandan suka kashe wasu na gaban kotu, wasu kuma na gaban irin wuraren da ake kai wannan koke.

Ya ce,"Saboda haka, ba za a samu wahalar samun irin wadannan mutane ba da kuma tantance su sannan ayi abin da ya dace ma'ana a bawa iyalansu hakkinsu".

Dan majalisar ya ce su kansu wadanda aka dauka a matsayin jami'an tsaro, suma mutane ne suna da nasu hakkin wadanda za a duba.

A wani labarin kuma, majalisar wakilan ta bukaci da a kafa ata hukuma mai zaman kanta da zata sanya idanu kan yadda za a gudanar da bincike tare da hukunta duka jami'an 'yan sandan na SARS da aka samu da laifin aikata irin wannan zalunci kan wadanda suke kamawa.

Wannan matakin na majalisar, kari ne a kan irin matakan da gwamnati ta dauka na rusa rundunar 'yan sandan ta SARS, da kuma alkawarin yin gyara ga hukumomin tsaron kasar.

Abin tambaya anan, shin ko wadannan matakai da aka dauka zasu iya kashe wutar zanga-zangar kin jinin 'yan sanda da ke ci gaba da bazuwa zuwa wurare daban-daban na Najeriyar?

Yan ƙasar dai suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa'ida ba da saɓa dokokin aiki.

A baya dai gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta soke rundunar ba, sai dai ta yi mata sauyi ko kuma kwaskwarima kan yadda rundunar ta ke gudanar da ayyukanta, inda ko a kwanakin baya sai da Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Ahmed Lawan ya ce ba zai yiwu a soke rundunar ba sai dai a sauya tsarinta.

A ranar 11 ga watan Oktoban, 2020 ne babban Sifeton 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami a Najeriya wato SARS.
Soke rundunar ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasar, inda ko a yau Lahadi sai da aka yi irin wannan zanga-zangar a Ingila.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)