Zakzaky na nan a raye - IMN



Kungiyar Harka Islamiyya ta 'yan Shi'a a Najeriya ta ce jagoranta Sheikh Ibraheem Zakzaky na nan a raye bai mutu ba.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta Ibrahim Musa ta ce, ya zama dole a gareta ta fito ta yi wa mutane bayanin kan jita-jitar da ake yaɗawa game da mutuwar jagoran nata.

Cikin sanarwar kungiyar ta ce, ta yi imanin cewa wasu 'yan kanzagin gwamnati ne suke yaɗa wannan jita-jita domin ƙara jefa Najeriya cikin wani ruɗani.

Sanarwar ta ƙara da cewa wani daga cikin iyalan Sheikh Zakzaky ya ziyarce shi a ranar Asabar 24/10/2020 a gidan yarin da ake tsare da shi a Kaduna.

Kowa ya sani Sheikh na fama da rashin lafiya mai barazana ga rayuwa sakamakon raunukan da ke jikinsa, wanda wannan ba baƙon abu ba ne, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa babu shakka wannan jita-jita ta fito ne daga gwamnati, da nufin ƙara gogawa kungiyar Harka Islamiyya ta 'yan Shi'a baƙin fenti, domin ƙara tayar da zaune tsaye.

Haka kuma ta ce tunda gwamnatin shugaba Buhari ta bijirewa umarnin babbar kotun tarayya na asaki jagoranta a 2016, to duk abin da ya faru ga Sheikh gwamnatin za su ɗorawa alhaki.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)