APC: Masu zanga-zanga da sunan #EndSARS su na da boyayyar manufa



- Mai Mala Buni ya yi tir da zanga-zangar #EndSARS da ake
yi a Jihohi
- Shugaban APC na rikon-kwarya ya ce akwai lauje a cikin
nadi a tafiyar
- Gwamnan Yobe ya ce za a iya samun matsala idan jama'a su
ka yi sake
Mukaddashin shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Mai
Mala Buni, ya tsoma baki a kan zanga-zangar #EndSARS da
ake ta faman yi.
Mai Mala Buni ya ce zanga-zangar da ake yi ta #EndSARS a
jihohin Najeriya, za ta iya kai wa ga barkewar rikici a fadin
kasar nan idan aka yi sake.
Gwamnan na Yobe wanda ke rike da jam’iyyar APC a matsayin
shugaban rikon-kwarya ya ce akwai wata boyayyar manufa a
wannan tafiya.
Buni ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi dazu a
gidan yada labarai na BBC Hausa a ranar Litinin, 19 ga watan
Oktoba, 2020, a shirin safe.
Zanga-zangar #EndSARS wanda ta yi sanadiyyar mutuwar
mutane a Najeriya ta fara ne da sunan fatali da dakarun da ke
yaki da masu fashi da makami.
“Miyagu za su iya amfani da wannan dama su kawo hatsaniya,
su rikita kasa, su tada hankalin jama’a.” Mai Mala Buni ya ke
fadawa BBC Hausa dazu.
Buni ya kara da cewa: “ Zanga-zangar da ake yi har yanzu ya
nuna akwai boyayyar manufa, bayan gwamnati ta yi na’am da
bukatun masu zanga-zangar.”

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)