Ku gaggauta rabar da duk tallafin korona da ku ka jibge a manyan shaguna - NLC ga FG, Jihohi



Ku rabar da duk tallafin korona da ke jibge a manyan
shaguna a fadin Najeriya - NLC ga FG, Jihohi

- Fusatattun batagarin matasa sun cigaba da balle manyan
shagunan ajiya na gwamnati tare da kwashe kayan abinci
- A makon da ya gabata ne matasa suka fara balle wani
babban shagon gwamnati a jihar Legas tare da yin awon gaba
da kayan tallafin korona dake ciki
- Tun bayan lokacin ake samun rahotannin balle manyan
shagunan da aka ajiye kayan tallafin korona tare da kwashesu
a sassan Najeriya
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci gwamnatin tarayya
da na jihohi su gaggauta rabar da duk wani sauran kayan
tallafin korona da ke suka jibge a manyan shagunan ajiya da
ke fadin kasar nan.
Kazalika, NLC ta yi Alla-wadai da barnatar da kayan tallafin
korona da wasu batagari ke yi har yanzu a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da NLC ta fitar ranar
Litinin mai taken, 'NLC ta bukaci a gaggauta raba duk wasu
kayan tallafin korona da sauran kayan agaji'.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)