Shugaban Senegal ya sallami ministocinsa 32

Shugaban Senegal Macky Sall, ya rushe majalisar ministocinsa, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

Gwamnatin tasa na da ministoci 32 da kuma sakatarori uku, kuma dukansu an sallame su.

Babu wani dalili da aka bayar na sauke ministocin, ko kuma lokacin da za a naɗa wasu sabbi.

A watan Maris ɗin shekarar nan ne Shugaba Sall ya lashe zaɓen shugaban ƙasar karo na biyu, sai dai 'yan adawa a ƙasar na zarginsa da daƙile wasu daga cikin manyan abokan hamayyarsa daga tsayawa takara.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)