An sanya dokar hana fita a jihar Adamawa
Gwamnatin jihar Adamawa ta sanya dokar hana fita biyo bayan lalata kaya da kuma yashe kayan abincin da ke cikin dakin ajiya na gwamnati da wasu ɓata gari suka yi.
Cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sanda na jihar DSP Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar, rundunar 'yan sanda ta jihar ta shawarci mutane da su mutumta kansu su bi wannan doka, domin kare faruwar irin wannan ɓarna a jihar.
Yayin da rundunar 'yan sanda ta jihar da sauran jami'an tsaro suka mutunta 'yancin al'ummar jihar, suna kuma shawartarsu da su guji aikata duk wani abu da zai iya jawo barazana ga tsaron jihar, in ji sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta ce babu yadda za a yi rundunar ta sanya idanu kan wasu ɓata gari suna aikata ɓarna ba tare da tsawatar musu ba, duk da cewa jami'anta sun yi aikinsu ta yadda ba a samu asarar rayuka ba yayin da suke hana satar da aka yi.
An kuma kafa wani kwamitin hadin gwiwa na duka jami'an tsaro da za su riƙa zagaye domin tabbatar da cewa al'umma sun bi dokar kamar yadda aka sanya ta.
Comments
Post a Comment