Gwamna Zulum ya ɗauki nauyin karatun 'ya'yan dakarun sa-kai da ke yaƙi da Boko Haram



Gwamnatin Jihar Borno ta ɗauki nauyin karatun 'ya'yan mayaƙan sa-kai da aka fi sani da Civilian JTF waɗanda suka rasa rayukansu yayin yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.

Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da hakan a Maiduguri, babban birnin jihar a yau Laraba yayin wani taro da ya tara dakarun sa-kai da ke taya sojoji yaƙi da 'yan bindiga Borno.

Borno
BSGCopyright: BSG
Kazalika gwamnan ya amince da bai wa matan waɗanda aka kashe ɗin naira 50,000 kowaccensu. Taron ya gudana ne a Jami'ar Jihar Borno.

Wata sanarwa da sashen yaɗa labaran gwamnatin Borno ya fitar ta ce gwamnan ya bai wa kowane mutum ɗaya naira 20,000 na mutum 9,000 da suka halarci taron.

Haka nan, an bai wa kowannensu buhun shinkafa ɗaya da kwalin taliya ɗaya da galan ɗin man girki.

Yaƙin Boko Haram wanda aka shafe tsawon shekara 10 ana yi, ya yi sanadiyyar kashe mutum fiye da 36,000 sannan ya tilasta wa miliyoyi tserewa daga mahallinsu.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)