Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki



Karfin hali ya kai wani matashi mai suna Kabiru shiga
majalisar dokoki sata
- Bai sani ba ashe na'urar CCTV na daukansa yayinda yake
satan
- Tuni an damke shi kuma an sanar da jami'an tsaron
majalisar dokokin dake Abuja
Wani matashi mai suna Kabiru a ranar Juma'a ya fasa cikin
majalisar dokokin tarayya inda ya shiga ofishin wani dan
majalisar wakilai ya kwashe daloli da wasu kayayyaki.
Wannan abu ya faru misalin karfe 2:30 na rana inda matashin
yayi amfani wani mukulli na daban.
An yi zargin Kabiru da kwashe daloli da kayayykin ofis irinsu
na'urar kwamfuta, na'urar fotocofi da printer.SaharaReporters ta tattaro cewa Kabiru ya kasance hadimi ga
wani dan majalisa daga Adamawa kuma sannanen mutum ne
a majalisar.
Jami'an tsaron majalisar sun gane fuskarsa a bidiyon na'urar
CCTV da ta daukeshi yana fashin.
A yayinda ake tattara wannan rahoton, wasu yan majalisa
wanda ya hada da mai magana da yawun mambobin majalisar
wakilai, Benjamin Kalu, na wajen da aka kama matashin.
An samu labarin cewa dan majalisar da matashin ke yiwa aiki
yana kokarin ganin an yi rufa-rufa kawai a manta da lamarin.
Bidiyon na'urar CCTV ya nuna matashin lokacin da yake satan.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)