Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami



Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara aiki kan rahoton bincike kan cin zarafin bil adama da ake zargin jami’an rundunar SARS da yi.

A shekarar 1994 ne aka kafa rundunar ta SARS mai yaki da fashi da makami a fadin kasar.

Sai da ‘yan kasar sun dade suna zargin jami’anta da aikata laifukan da suka hada da mugunta, cin zarafin biladama da kisa ba tare da gurfanarwa a gaban kotu ba.

A hirarsu da BBC, Ministan Shari’a na Najeriyar Abubakar Malami ya ce a jiya ne hukumar kare hakkin bil adama ta kasar ta mika masa rahoton kan binciken da ta yi game da jami’an kuma tuni ya soma aiki a kansa.

Game da tsawon lokacin da aka dauka kafin kwamitin ya mika rahoton nasa, Ministan ya bayyana cewa a tsarin gwamnatin kasar, idan aka gabatar mata da zargi ko koke-koke irin wadannan da ke da nasaba da cin zarafin bil adama, dole ne sai ya dauki tsawon lokaci ana bin bahasi kafin a cimma bukatar da ake da it ana binciko ainin wadanda suka aikata laifin.

‘’A karkashin Hukumar kare hakkin biladama ta kasa, mun kafa kwamiti na tsawon lokaci don ya bi bahasin wadannan koke-koke, ta kuma kamala aikinta, kuma a jiya ta gamsu da rahoton binciken wadannan kokoe, kuma ministan shari’a ya karbi wannnan rahoto za kuma za a duba a ga irin hukuncin da ya kamata a dauka’’, ya ce.

A baya dai ana ta bayyana cewa za a sallami wadannan jami’ai na rundumar ta SARS daga aiki. Amma kuma ministan ya ce gwamnati ba za ta yi riga malam masallaci ba wajen yanke hukunci sai an gama bin diddigin rahoton.

Baya ga rushe rundunar ta SARS, daya daga cikin bukatun masu zanga-zanga dai shi ne duk wanda aka samu aikata laifi a cikin jami’an nata a sallame shi daga aiki.

Ita kan ta hukumar ‘yansandan kacokan in ji ministan, kacokan shugaban kasa ya taba saka wata doka wacce ta ke da nasaba da aikin dansanda hannu, wacce akwai gyare-gyare da suka shafi inganta rayuwar ‘yansanda , fuskantar mu’amalar taro ta aikin dansada daga bangaren al’umma da sauransu.

‘’Idan za ka iya tunawa a shekarar 2019 ne gwamnati ta kafa wata doka wacce za ta duba yadda za samarwa da ‘yansanda kudade na yin maganin damuwar da suke da ita, kama daga albashi, kayan aiki da makamantansu’’.

‘’Za mu zauna mu bi bahasi, zamu dau matakai na gaggawa , akan tasri na aiki mu ga cewa an cikin kankanin lokaci an yi abinda ya kamata’’.

An dai dade ana zargin ‘yansandan Najeriyar da aikata laifukan karbar cin hanci da rashawa, cin zarafin bil adama, da sauran laifuka da suka shafi aikata ba daidai ba a kasar. Lamarin da masu sharhi kan al’amuran da suka shafi tsaro a kasar ke cewa yana da nasaba da rashin inganta rayuwar aikin dansanda a kasar.





Comments

Popular posts from this blog

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau