EndSARS: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS



Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta ce ta kwace makaman
da ke hannun jami'an sashen dakile fashi da makami FSARS
na jihar

- Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu ya
bayyana hakan, yana mai cewa, yanzu an rushe sashen
jami'an, ba sa kara yin aiki

- Haka zalika, ya karyata rahotannin cewa an kashe wami mai zanga zanga a Surulere a ranar Litinin, yana nuni da cewa,
dan kallo ne aka kashe Kwamishinan 'yan sandan jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya
ce bi umurnin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda,
Mohammed Adamu, na ruguza sashen rundunar SARS.

Odumosu, wanda ya gana da wasu lauyoyi da suke zanga
zanga kan cin zarafin da jami'an SARS ke yiwa jama'a, ya ce
tuni aka kwace makamai daga hannun jami'an rundunar SARS

Odumosu, wanda ya jinjinawa masu zanga zangar bisa
jagorancin lauyan kare hakkin bil Adama, Inibehe Effiong, na
nuna dattako, ya kuma ce babu mutum daya da aka kashe a
zanga zangar jihar.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)