Yanzu-yanzu: An umurci dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya su koma aiki

Gwamnatin tarayya ta bada umurnin dukkan ma'aikata
manya da kanana su koma aiki ranar Litinin
- Sanarwar ta fito ne daga bakin hukumar shugaban kasa ta
yaki da annobar korona, PTF, a ranar 15 ga watan Oktoba
- Amma PTF ta umurci ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin da
ke karkashin FG su raba ranakun da ma'aikatan za su rika
zuwa aiki don gudun cinkoso

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati
da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma
aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.
Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF,
Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da
haka yayin taron manema labarai ranar Talata.
Ma'aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da waɗanda ke
yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki.
Amma PTF ta umurci ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin da
ke karkashin FG su raba ranakun da ma'aikatan za su rika
zuwa aiki don gudun cinkoso
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati
da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma
aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.
Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF,
Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da
haka yayin taron manema labarai ranar Talata.
Ma'aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da waɗanda ke
yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki.
Amma a yanzu PTF ya umurci dukkan ma'aikata na ƙasa da
mataki na 12 su koma bakin aiki.
Amma duk da haka ta umurci ma'aikatu, hukumomi da
cibiyoyin da ke karkashin gwamnati su raba ranakun da
ma'aikatan za su rika zuwa aiki don gudun cinkoso.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)