Allah Ya yi wa Sanata Saidu Umar Kumo rasuwa da safiyar yau Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020. Tsohon sanatan wanda ya wakilci mazabar Jihar Gombe ta Tsakiya, ya rasu ne a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya. Kafin rasuwarsa, shi ne Garkuwan Gombe. Ya riƙe shugaban kamfe ɗin Alhaji Atiku Abubakar a shiyyar arewa maso gabas a zaɓen shugaban ƙasa na 2019. Sai dai Sanata Kumo ya koma jam'iyyar APC mai mulki a watan Janairun 2019 kafin a shiga zaɓen da Muhammadu Buhari ya lashe a watan Fabarairu. An zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa a shekarar 1999 zuwa 2003 kafin daga baya ya yi takarar gwamnan Gombe a 2011, inda ya sha kaye a hannun Ibrahim Hassan Dankwambo. Za a yi jana'izarsa a Masallacin Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:00 na rana.
Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau. Sakon da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Twitter, ya ambato Gwamnatin jihar na cewa "Gwamnatin jihar kaduna ta sanar da nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19. Ya mayer gurbin Mai Martaba Alhaji (Dr.) Shehu Idris wanda ya rasu ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2020, bayan ya kwashe shekara 45 yana kan mulki."
Comments
Post a Comment