Da duminsa: IGP ya janye 'yan sanda masu tsaron dukkan manyan mutane a Najeriya



Shugaban 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya
bada umarnin janye 'yan sanda masu kare lafiya
- Ya umarci janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar
manyan mutane a fadin Najeriya a yau Laraba
- Gidajen gwamnatoci, shugaban majalisar dattawa da
kakakin majalisar wakilai kadai aka amince a basu kariya
Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu,
ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar
manyan mutane a fadin kasar nan.
Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan
bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a
tituna.
Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga
dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin
wanda
A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati,
shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar
wakilai ne aka tsame.
"Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada umarnin janye
dukkan 'yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na
gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kakakin
majalisar wakilai," sakon yace.
"Duk wani kwamandan da ya saba wannan dokar zai fuskanci
hukunci. Duk wani jami'in tsaro da aka kama yana tsaron wani
babban mutum da makami ko babu, za a sauya masa wurin
aiki kuma za a hukunta kwamandansa."
An umarci dukkan 'yan sanda masu tsaron da aka janye da su
gaggauta zuwa gaban kwamandansu.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)