Ƴan Najeriya miliyan 79 ke cikin matsanancin talauci a 2018 - Bankin Duniya



Wani sabon rahotan Bankin Duniya ya ce Najeriya ce ƙasa mafi
yawan matalauta a ƙasashen kudu da hamadar sahara, wanda
ƴan ƙasar miliyan 79 a 2018 ke cikin matsanancin talauci.
Najeriya ke da kashi 20 cikin 100 na matalauta a yankin, kamar
yadda rahotan bankin kan talauci ya nuna.
Sannan rahoton ya kara da cewa annobar korona za ta sake
tursasa wa mutum miliyan 40 shiga matsanancin ƙangin
talauci a kudu da hamadar sahara.
Ya ce, "Kusan rabin mutanen da ke cikin talauci a kudu da
hamadar saharar Afirka na rayuwa ne a ƙasashe biyar da suka
hada da Najeriya da DR Congo da Tanzania da Ethiopia sai
kuma Madagascar.
"A Najeriya, yankunan arewaci talaucin ya fi kamari, yayinda a
yankunan kudu da garuruwan bakin ruwa abin da dan sauki."
Bankin duniya ya ƙiyasta cewa annobar Covid-19 za ta sake
jefa karin mutum miliyan 88 zuwa 115 cikin matsanancin
talauci a wannan shekarar, adadin da ya ƙiyasta zai karu zuwa
miliyan 150 a 2021, ko da yake ya danganta na yanayin tattalin
arzikin ƙasashe

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)