Masu Fafutukar Biafra sun kashe mutane ‘yan Arewa 30, sun lalata motocin bas 50, da tirela damanyan motocin ‘yan arewa – In Ji Ƙungiyar tuntuba ta Arewa.



Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kuka kan zargin kashe
wasu ‘yan arewa a yankin Kudancin kasarnan.

Taron ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta ta nemi gwamnatocin jihohi daban-daban da su kafa kwamitocin
bincike kan zargin kashe-kashen ‘yan Arewa.Sakataren yada labarai na ACF na kasa, Emmanuel Yawe a
cikin wata sanarwa a Kaduna ya ce ya samu rahoto daga shugabanta na jihar a Jihar Ribas, Alhaji Ibrahim Tukur Tudunwada cewa ’yan Arewa da ke zaune a jihohin Ribas da Abia mambobin haramtattun yan asalin Biafra suna yin garkuwa da su.

Ta yi zargin cewa kimanin ‘yan arewa 30 aka kashe, yayin da
bas-hamsin, tirela da manyan motocin’ yan arewa a jihohin da
kungiyar IPOB ta lalata.

Sanarwar ta ruwaito shugaban ACF na jihar, Alhaji Tudunwada
yana yabawa gwamna Wike saboda hana ayyukan kungiyar
IPOB a cikin jihar.

Sanarwar ta lura cewa wadanda suka tsira daga harin sun
kasance cikin tsoro na har abada na barazanar rayuwarsu.ACF ta gargadi ‘yan arewa da ke shirin tafiya zuwa Kudu don yin watsi da irin wadannan shirye-shiryen, yayin da ta yi kira ga Shugaba Buhari da ya dauki kwararan matakai domin ceton rayukan dukkan‘ yan Najeriya a duk inda suke.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau