Fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin Benin sakamakon zanga-zanga




A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa wasu matasa da ke zanga-zanga sun balle gidan yari a Benin, jihar Edo - Rundunar 'yan sanda ta ce ba za ta lamunci tashin hankali ba ganin yadda aka samu gurbatattu a cikin masu zanga zangar ENDSARS - Ana zargin ma su zanga-zanga da tafka barna, su kuma ma su zanga-zanga na zargin an yi hayar batagari don su bata musu zanga-zanga Hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya (NCS) ta tabbatar da cewa fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin da ma su zanga-zanga su ka balle ranar Litinin a Benin, jihar Edo. Legit.ng Hausa ta rawaito yadda wasu batagarin matasa su ka balle wani gidan yari da ke kan titin Sapele a birnin Benin da safiyar ranar Litinin. Sakamakon hakan, gwamnatin jihar Edo ta sanar da saka dokar ta baci ta sa'a 24. A cikin wani jawabi da NCS ta fitar ranar Talata ta hannun darektan yada labarai da hulda da jama'a, Mohammed Manga, hukumar ta bayyana cewa ''ma fi yawan ma su laifin da su ka tsere wadanda ke jiran mutuwa ne bayan an yanke mu su hukunci kisa. 

fursuna-1993-sun-tsere-daga-gidan-yarin-benin-sakamakon-zanga-zanga.


Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)