An raunata wani mai gadi a ofishin jakadancin Faransa a Saudiyya


An kama wani mutum a birnin Jidda na kasar Saudiyya da ake zargi da raunata wani maigadi a ofishin jakadancin Faransa da ke birnin, ta hanyar daba masa wuka.

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani a kan abin da ya haddasa harin.

Sai dai harin ya biyo bayan zaman dar-dar din da ake yi a gabas-ta-tsakiya, sakamakon matsayin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya dauka na kare zanen batancin nan da aka yi na aibanta Annabi Muhammadu.

Tuni dai Ofishin ofishin jakadancin Faransar ya gargadin Faransawa mazauna Saudiyya da su dinga taka-tsantsan.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)