Yan bindiga sun kashe wani basarake a Kaduna



Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe Mai Garin Runji Alhaji Musa Abubakar.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun afka gidansa ne da sanyin safiyar Lahadi a garin na Runji da ke Ƙaramar Hukumar Ikara ta Jihar Kaduna.

Jaridar ta ruwaito cewa ɗan mai garin, Suleiman Musa wanda shi ma mai gari ne a ƙauyen Rafin Rogo, shi ya tabbatar musu da wannan labari.

Haka zalika Kantoman Ƙaramar Hukumar Ikara, Salisu Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kai jami'an tsaro ƙauyen na Runji tare da tabbatar da cewa za a gano waɗanda suke da hannu a kisan mai garin kuma a hukunta su.

Article share tools



Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)