Sarauniya Amina: Jarumar da ta yi mulkin shekaru 34 a masarautar Zazzau



Babu shakka kasar Zazzau ta taba samun wata jarumar
Basarakiya da ake kira da sarauniya Amina

- Ta jagooranci maza zakakurai kuma dakarun yaki har
20,000 bayan watanni da hawanta karagar mulki

- Sarauniya Amina gagarumar basarakiya ce da ta kwashe
shekaru 34 tana mulki kuma ta fadada arzikin masarautarta
Idan har za a yi zancen mata jarumai a Najeriya, ba za a taba
mantawa da sarauniya Amina ta Zazzau ba.

Jarumar basarakiyar ta jagoranci rundunar yaki ta maza kuma ta kwato
yankuna da yawa a kusa da kasar Zazzau.

Kamar yadda rahoto ya nuna, basarakiyar an haifeta a gidan
hamshakin basarake, Sarki Bakwa na Turunku a shekarar 1533
kuma a Zazzau suka rayu.
Gidansu manyan masu arziki ne domin su ke siyar da tufafi,
gishiri, goro, karfe da kuma dawakai.

A zamanin mahaifinta, Amina tana samun horon yaki daga
sojojin Zazzau, hakan ne ya gogar da ita sosai wanda daga baya ta zama shugaban mayakan.
Sarauniya Amina

Jarumar da ke kashe duk namijin da ya kwanta da ita. Hoto daga Tumblr.

Sarki Bakwa na Turunku ya rasu a 1566 kuma dansa Karama shine ya gajesa. 

Ya rasu bayan kwashe shekaru 10 yana mulki.

A zamanin Karama, Amina ta zama fitacciyar mayakiya kuma ta zama sarauniya bayan rasuwarsa.

Sarauniya Amina ta jagoranci mayakanta a karon farko bayan
watanni kadan da zamanta sarauniya. 

Ta yi wa dakaru kusan
20,000 jagora zuwa yaki.

Jarumar sarauniyar ta samowa masarautarta arziki mai tarin
yawa domin ita ta fara yi wa mayakanta sulken yaki.

Sarauniya Amina bata taba aure ko haihuwa ba. Kamar yadda
Face 2 Face Africa ta wallafa, tana kwanciya da mazan da ta
samo matsayin ganima sannan sai ta kashesu washegari domin tsare sirrinta.

Ta kashe kanta ne bayan da ta kwanta da wani mutumi amma
yayi nasarar tserewa washegari. Jama'a suna kwatanta da mace mai kamar maza.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)