Abin da ake sa ran Buhari zai gabatar wa majalisa na kasafin kuɗin 2021


..

A ranar Alhamis ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2021 gaban Majalisar Tarayyar ƙasar.

Sai dai kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Barau Jibril ya bayyana, gabatar da kasafin kuɗin na wannan shekarar zai sha bamban da na sauran shekaru sakamakon annobar cutar korona.

A cewarsa, za a bi ƙa'idojin kare yaɗuwar cutar da kuma yin tanadi ta yadda ba za a samu cunkoso ba yayin gabatar da kasafin kuɗin, hakazalika ba za a daɗe wurin gabatar da kasafin kudin ba kamar yadda ake yi ba a da.

An dai ɗora ƙudurin kasafin kuɗin na 2021 kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 379 da kuma mizanin gangar man fetur guda a kan dala 40, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 1.86 a kullum.

A bara dai an amince da kasafin kudin ne kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 305, haka kuma an saka mizanin gangar man fetur guda a kan dala 57, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 2.18 a kullum.

Ana sa ran shugaban yayin gabatar da kasafin kuɗin a ranar Alhamis, zai nanata wasu kalaman ministar kuɗin ƙasar wadda ta bayyana cewa ƙudirin kasafin 2021 yana cike da burin bai wa ƙasar damar samun bunƙasa ta kowane ɓangare da kuma zaburar da tattalin arziƙin Najeriya da samar da ayyuka.

Kalaman nata sun kuma haɗa da yauƙaƙa bunƙasar ƙasar, da samar da hanyoyin zuba jari ga ababen more rayuwa, da inganta masana'antu da sana'o'in cikin gida.

Ana sa ran wannan kasafin kuɗin na 2021 zai jaddada hasashen samun jumullar kuɗin shiga naira tiriliyan 7.89 da kuma ƙunshin kasafin kamfanoni 60 mallakar gwamnati.

A bara dai, Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2020, wanda ya kai naira tiriliyan 10,594,362,364,830.

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)