Sojojin Turkiyya na gwajin makami mai linzami duk da hanin da Amurka ta yi



Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tabbatar cewa sojojin kasar suna gwajin makami mai linzami samfurin S-400 da Rasha ta ƙera duk da cewa Amurka ta nuna rashin amincewarta.

Kafafen yada labarai a Turkiyya sun rawaito cewa an yi gwajin farko a makon daya gabata a Lardin Sinop.

Amurka dai ta yi kakkausar suka game da lamarin.

Wakilin ma'aikatar tsaron Amurka ya ce irin wadannan gwaje-gwajen ba za su yi dai-dai da alƙawuran da Turkiyya ta ɗauka ba a matsayinta na ƙawar Amurka da ƙungiyar tsaro ta NATO.





Comments

Popular posts from this blog

Buhari ya ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba

KUDUQUFA WAJAN ADU'O'I ~Shugaban Kungiyar ZASDA Yayi Kira

Association with the company and the