Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja
Zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS ta fara sauya salo a sassan Najeriya da ta samu karbuwa
- Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa ana yawan samun kai hari a kan ma su zanga-zangar adawa da ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da alaka da kowacce zanga-zanga An fito da dakarun soji zuwa kan titunan Abuja domin shawo kan zanga-zangar ENDSARS da ta fara sauya salo.
Zanga-zangar ENDSARS a Abuja ta fara sauya salo tare da neman rikidewa zuwa rikici sakamakon harin da wasu batagari ke kaiwa ma su zanga-zangar.
Batagari a Abuja na kai hari kan ma su zanga-zangar nuna adawa da rundunar SARS da kuma ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS. Lamarin, a yawancin lokuta, ya haddasa gumurzu tare da zama sanadiyyar raunata mutane da kuma lalata dukiya. sauya-salon-zanga-zanga-an-sako-sojoji-zuwa-titunan-abuja.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin ma su zanga-zanga ya rasa ransa a asibitin da aka kai shi sakamakon mummunan rauni da wasu batagari suka yi masa a Abuja. An ga dakarun soji da safiyar ranar Litinin a sanannen shataletalen AYA, wurin da masu zanga-zanga su ka yi niyyar mamayewa.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa an ga dakarun soji sun saka garkuwa a kan titin domin tabbatar da cewa ma su zanga-zangar basu
A jiya, Lahadi, ne rundunar soji ta sanar da cewa sabon atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da wata nasaba da zanga-zangar da matasa ke yi a kan rushe rundunar SARS da zaluncin 'yan sanda.
A cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar (DHQ), kanal Sagir Musa, kakakin rundunar soji ya ce kuskure ne a bayyana cewa an kaddamar da atisayen ne saboda zanga-zangar ENDSARS da ake yi a sassan kasa. Kanal Sagir ya bayyana cewa rundunar soji ta nuna kwarewar aiki tun bayan barkewar zanga-zangar kusan sati biyu da su ka wuce.
Comments
Post a Comment