Gwamnan Ribas ya shiga cikin masu zanga-zanga bayan ya haramta #EndSARS



Nyesom Wike ya shiga cikin masu zanga-zangar #EndSARS
a Fatakwal
- Gwamnan ya lashe aman da ya yi na cewa ba zai bari ayi
zanga-zanga ba
- Wike ya ce dama tun farko ya na cikin wadanda su ke
adawa da F-SARS
A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, 2020, gwamna Nyesom
Wike na jihar Ribas ya lashe amansa na haramta zanga-zangar
da ake yin a #EndSARS.
Mai girma Nyesom Wike ya shiga cikin sahun masu wannan
zanga-zanga, har kuma ya yi kira da a yi wa hukumar ‘yan
sandan Najeriya garambawul.
Gwamnan ya yi wannan ne bayan kwana guda da fitar da
jawabi inda ya ce ba zai yarda da zanga-zanga a jiharsa ba,
ganin cewa IGP ya rusa SARS.
Da ya ke jawabi a gaban masu zanga-zangar, Wike ya ce ko da
ya ke ba goyon bayan abin da jama’an su ke yi, ya na cikin
masu sukar aikin ‘yan sanda.
Gwamna Wike ya ce babu gwamnan da ya kalubalanci jami’ar
tsaro kamar yadda ya yi a baya.
“Ba na goyon bayan mu zo nan. Na rantse zan kare lafiya da
dukiyoyin mutanen jihar Ribas. Jinanan jihar Ribas ya na da
daraja a wurina.” inji gwamnan.
Ya ce: “Ribas ta sha wahala a hannun SARS. Lokacin da mu ka
fallasa danyen aikin da SARS su ke yi, ba a kulamu ba, yanzu
aikinsu ya bulla a wasu wurare.”
Babu gwamna a kasar nan da ya kalubalanci SARS kamar
yadda mu ka yi. Lokacin da ake yawon garkuwa da mutane, na
kai kuka wajen gwamnatin tarayya.”
Wike ya ce shi kadai ne gwamnan da ya fita zanga-zangar a
doke SARS. “Mun rasa mutane rututu saboda SARS a nan.
Babu jihar da ta mara mana baya.”

Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)