Ga Jerin Manyan nasarorin DCP Abba Kyari Hamisin 50 daga cikin dari da Hansin 150

ALLAHU AKBAR: Ga Jerin Manyan nasarorin DCP Abba Kyari Hamisin 50 daga cikin dari da Hansin 150 da zan kawo maku..

 ~Shine 'dan Sanda Mafi kama 'yan ta'adda a duk tarihin Nageriya...
S
1 KAMA: shahararren mai garkuwa da mutanen Najeriya mai suna Chukwudumeme Onwaumadike Aka ‘Evans’ a jihar Legas Wanda aka kama tare da tawagarsa wanda yanzu haka ake kan shari’a.

2 KAMA: wadanda suka kashe tsohon Babban Hafsan Tsaro (CDS) Air Marshal Alex Badeh ‘rtd’ a kan hanyar Keffi-Gitata Kaduna, shima yanzu Shari’a ke tuhumarsu.

3 KAMA: kwamandan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo Umar Abdulmalik tare da mutun Takwas (8) 'yan kungiyar ta'addancinsa shima ana kan bincike.

4 KAMA: 'yan ta'addar Boko Haram ashirin da biyu (22) da suka yi garkuwa da' yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014 sannan kuma su ke da alhakin jerin hare-haren kunar bakin wake/hare-hare da dama da kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Shima shari'ar na kan tuhuma.

5 KAMA:  wanda ya fi kowa yawan yin garkuwa da mutane a tarihin Najeriya, Henry Chibueze Aka “Vampire” da ‘yan gungunsa a Owerri, Jihar Imo, shima Yana karkashin shari’a.

6 KAMA: munanan yan fashin bankin Offa da suka mamaye garin Offa, ta jihar Kwara suka yi fashi a Bankunan kasuwanci guda biyar, kungiyar ta kuma kashe 'yan Najeriya talatin da daya (31) wadanda ba su ji ba ba su gani ba..

7 KAMA: masu garkuwa da mutane, wadanda suka yi garkuwa da Mataimakin Kwanturola na Kwastam a Fatakwal, Jihar Ribas, shima yana karkashin tuhuma.

8. KAMA:  wani gungun masu garkuwa da mutane, 'yan fashi da makami da masu daukar nauyin su a jihar Zamfara, bayan da' yan kungiyar suka yi garkuwa da 'yan uwa ​​tagwayen kafin bikin auren su, lamarin da ke karkashin tuhuma Yanzu.

9. KAMA:  muggan 'yan fashi da makami da masu kisan kai da suka tsere daga hannun SARS Lokoja, A Jihar Kogi, Al'amarin na karkashin tuhuma Yanzu.

10 KAMA: masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da Mista John Iheanacho ma’aikacin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC)/Shugaban Kungiyar Masu Zuba Jari na Yankin Gabas, a Fatakwal, Jihar Ribas, Lamarin na karkashin shari’a Yanzu.

11 KAMA: wanda ake zargi da alhakin kisan Laftanar Abubakar Yahaya Yusuf jami'in Sojojin Ruwa da budurwarsa Miss Lorraine Onye a jihar Ribas, shari'ar itama ana kan tuhuma.

12 KAMA:  masu garkuwa da mutane da ke da alhakin garkuwa da wasu 'yan asalin Afirka ta Kudu biyu a jihar Kaduna, wanda lamarin ake tuhuma Kan laifin.

13 KAMA: 'yan ta'adda da ke da alhakin tashin bam a garuruwan Kuje da Nyanya na Abuja da kuma dawo da wasu bama -bamai a cikin babban birnin tarayyar Abuja, yanzu haka shari'ar itama na Kan tuhuma.

14 KAMA:  masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da Amurkawa biytuhumaShinn Kanada biyu a jihar Kaduna, shari'ar  na kan tuhumaSh

 15 KAMA:  wani shahararren mai laifi da ke barazanar kashe tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da Iyalansa lamarin na kan shari'ar da ake tuhuma Yanzu.

16 KAMA: masu garkuwa da dattijon Cif Olu Falae a jihar Ondo, an yanke wa wadanda ake zargi hukuncin daurin rai da rai a babbar kotun jihar Ondo.

17 KAMA:  gungun masu kisan gilla da ke da alhakin kashe mutane da dama da ba su ji ba ba su gani ba a jihar Benue da kwato makamansu na ta'addanci, lamarin shari'ar da ake tuhuma.

18 KAMA: shahararren dillalin makamai wanda ya kware wajen siyar da makamai ga yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane a Kudu maso Yamma/kwato makamai fiye da hamsin da dubban harsasai masu rai da motsi, yanzu shari'ar ana kan tuhuma.

19 KAMA:  babban mashahurin ɗan fashi da makami a yankin Kudu maso Yamma, Abiodun Egunjobi Aka “Godogodo” a Ibadan, Jihar Oyo, shi ne ya yi sanadin mutuwar sama da mutun ɗari biyar (500) ’yan Najeriya ciki harda Jami’an’ yan sanda marasa laifi, shima shari’ar yanzu haka ana kan tuhuma.

 20 KAMA:  masu garkuwa da 'yan matan Makarantar Turkawa a jihohin Ogun da Legas, shari'ar da yanzu haka ake tuhuma,

21 KAMA:  masu garkuwa da mutane da suka kashe Barista Sherif Yazid a kan hanyar Abuja-Kaduna Express, itama karar yanzu haka ana kan tuhuma,

22 • KAMA: mafi Shahara kuma sarkin masu garkuwa da mutane a jihar Kogi Halti Bello da mutun ashirin daga cikin gungun mutanen sa, kungiyar ta dade tana addabar jihar Kogi da kewayenta, sannan kuma ta yi garkuwa da wani Mai suna Istifanus Gurama wani babban ma’aikacin rukunin kamfanin Dangote. Shima Yana  karkashin tuhuma.

23 • KAMA:  sama da kungiyoyi ashirin (20) daban-daban na masu garkuwa da mutane sama da dari uku (300) da kwato bindigogi AK-47 sama da dari biyu (200) da sauran muggan makamai da aka yi amfani da su wajen tsoratar da manyan hanyoyin Abuja-Kaduna-Kano, lamarin shima na karkashin tuhuma yanzu:

24.

25 • KAMA:  babban mashahurin mai kisan kai a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan Ade Lawyer da gungun 'yan kungiyar sa da ke da alhakin kashe-kashen mutane a sassa daban-daban na Jihar Legas da Kudu maso Yammacin Najeriya, wanda shima yanzu ake tuhuma da laifin.

26 • KAMA:  masu garkuwa da masu gidan haya na Isheri a jihar Legas, shima shari'ar na kan tuhuma.

27 • KAMA: masu garkuwa da Cif Felix Ogbona mai shekaru tamanin (80) a Aba ta, jihar Abia, shima na karkashin tuhuma Yanzu.

28 KAMA: masu kisan gilla da masu hannu da shuni da suka kashe Mr. Uba Emmanuel wanda aka fi sani da 'Onwa' a Garin Festac, Jihar Legas, Shima lamarin na karkashin tuhuma.

29 KAMA: mashahuran masu garkuwa da mutane da ke da alhakin yin garkuwa da Dr. Alex Pepple a Fatakwal na Jihar Ribas, Shima na  karkashin tuhuma.

30 • KAMA: masu garkuwa da 'yan matan makarantar Ikorodu a jihar Legas, shima lamarin na karkashin shari'ar da ake tuhuma yanzu.

31 • KAMA: masu garkuwa da matar Gwamnan CBN a jihar Delta, Shima lamarin na karkashin shari’ar da ake tuhuma Yanzu.

32 KAMA: masu garkuwa da Ambasada Bagudu Hirse a jihar Kaduna, lamarin na karkashin shari'ar da ake tuhuma.

33 • KAMA:  masu garkuwa da mataimakin babban kwamishina Serrie-Leonian a jihar Kaduna, shari'ar da yanzu ake tuhuma.

34 • KAMA: masu garkuwa da mahaifiyar tsohuwar Ministar Kudi Okonjo Iweala a Jihar Delta, Shima lamarin na karkashin shari’ar da ake tuhuma.

35 KAMA: 'yan bindigar Neja-Delta dake  shirin tayar da bam a gadar 3rd Mainland da kwato makamai da abubuwan fashewa a jihar Legas, shari'ar da ake tuhuma itama.

36 • KAMA 'yan bindigar Neja Delta/sanannen masu garkuwa da mutane tare da kwato bindigar GPMG, AK-47 da gurneti na soji a Fatakwal, jihar Ribas, shari'ar da ake tuhuma Yanzu.

37 • KAMA:  shahararren gungun 'yan bindiga da suka yi shirin yin garkuwa da hamshakin attajirin nan na Najeriya Mista Femi Otedola a jihar Legas, wanda Suma yanzu ake tuhuma da laifi.

38 • KAMA:  masu garkuwa da Oniba na Iba wani Sarki mai daraja ta daya a jihar Legas, shi ma dai lamarin  shari'ar da ake tuhuma.

39 • KAMA: masu garkuwa da mutane da sukayi garkuwada Hon. Sani Bello dan majalisar
 Wakilci/mai wakiltar Mazabar Mashi ta Jihar Katsina karar ce da yanzu ake tuhuma.

40 • KAMA  'yan fashi da makami/militants)  da suka kai farmaki tare da yi wa Bankunan Lekki, Ikorodu, Festac da Agbara a jihar Ogun da jihar Legas lamarin shari'ar da ake tuhuma Yanzu.

41 • KAMA masu garkuwa da yaran Orekoya (3) uku a jihar Legas, shari’ar da ake tuhuma Yanzu haka.

42  KAMA masu garkuwa da tsohon Shugaban karamar hukumar Ejigbo a jihar Legas, shari'ar da ake Kan tuhuma.

43 • KAMA: wadanda suka kashe dan majalisar dokokin jihar Oyo a jihar Oyo, karar da ake tuhuma itama.

44 • KAMA: masu garkuwa da mutane da kuma kashe Reverend Father Adeyi a Otukpo jihar Benue, wanda babban kotun jihar Benue ta yankewa hukuncin kisa.

45 • KAMA: gungun wasu sanannun masu garkuwa da mutane na Alhaji Salami a Abuja, shari'ar da ake kan tuhuma,

45b: KAMA: mutane biyar (5) da suka yi garkuwa da ma'aikatan Gidan Talabijin na Channels a Abuja, shari'ar da ake kan bincike haryanzu.

46 • KAMA:  masu garkuwa da dalibai mata (2) na Jami’ar Amurka ta Najeriya ta ABTI da ke Abuja, wanda ake tuhumarsu Yanzu haka.

47 • KAMA: mahara da masu kashe Al'ummar Nimbo a Jihar Enugu, shari'ar da itama ake kan tuhuma.

48 • Ceto Magajin Garin Daura daga masu garkuwa da mutane a jihar Kano da kuma kame mutum goma sha uku (13) na masu garkuwa da mutane/'yan ta'adda, haryanzu ana kan binciken su.

49 • KAMA: wani mashahurin sarkin garkuwa da mutane na yankin Kudu maso Yamma Abubakar Moh'd Aka ‘Buba’ da ‘yan Gang a Jihar Oyo, shari’ar da ake kan bincike haryanzu.

50 • KAMA: wanda ya fi kowa yin garkuwa da mutane a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya Abdullahi Abubakar da aka fi sani da ‘Osama’ da kungiyarsa a Jihar Ekiti, shari’ar da ake kan bincike haryanzu...

Rubutun zai cigaba zuwa nasarorinsa guda dari da Hamisin rubutawar fassara marubuci Malam M Inuwa MH...



Comments

Popular posts from this blog

Za a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi a rundunar SARS - Malami

An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)