Duba da shekaru da nauyinsa, korona na barazana ga rayuwar Trump Ƙarin bayani a nan:


Donald Trump na fuskantar haɗurra daban-daban da suka haɗa da nauyi da shekarunsa - waɗanda ka iya ta'azzara jinyar cutar korona da yake yi yanzu haka.

Shekarun haihuwarsa 74 sannan yana da girman jiki fiye da 30 a ma'aunin Body Mass Index (BMI).

Ya zuwa yanzu Trump na fuskantar ƙananan alamun cutar ne, yayin da ake kula da shi da ƙwayoyin da ke rage raɗaɗin cutar a jikin ɗan Adam.

Sai dai yawan shekaru babbar barazana ce da ka iya ta'azzara cutar har a je asibiti, a wasu lokutan ma har da mutuwa.

"Sai dai mafi yawan waɗanda ke kamuwa da cutar na warkewa," in ji Dr Bharat Pankhania na Jami'ar Exeter a hirarsa da BBC.

Wasu bincike da aka yi fiye da 100 a faɗin duniya sun nuna cewa haɗarin da ke kan matasa da ƙananan yara na cutar ba shi da yawa.

Sai dai daga cikin 'yan shekara 75, duk mutum ɗaya cikin 25 na waɗanda suka kamu da cutar na mutuwa.

Comments

Popular posts from this blog

Buhari ya ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba

KUDUQUFA WAJAN ADU'O'I ~Shugaban Kungiyar ZASDA Yayi Kira

Association with the company and the