Coronavirus: Abin da zai faru idan rashin lafiyar Trump ta yi tsanani
Wannan lamarin ya haifar da jerin tambayoyi game da abin da zai iya faruwa a kasar.
Wadanne gangamin siyasa shugaban zai fasa halarta?
Ana bukatar shugaba Trump ya killace kansa na kwana 10 daga ranar da ya karbi sakamakonsa na cewa ya harbu da cutar. Saboda haka yana iya halartar muhawara ta gaba da aka shirya yi ranar 15 ga watan Oktoba.
Amma an soke wani gangami da aka shirya yi a jihar Florida. A madadin haka shugaban zai buga waya daga Fadar White House ga dattawa irinsa masu raunin kiwon lafiya.
Akwai kuma wasu tarukan na siyasa da aka shirya gudanarwa, amma babu makawa tilas a soke su ko a ɗage su zuwa wani lokaci.
Wane dalili ne zai sa a jinkirta gudanar da zaben?
Killace kansa da shugaban ya yi zai yi tasiri kan damar da yake da ita ta yin kamfe.
Saboda haka ake tambayar ko za a iya jinkirta zaben, kuma ya hakan zai kasance?
A karkashin dokar Amurka, a kan yi zabe ne a ranar Talatar da ke bin Litinin ta farko a watan Nuwamba, a kowace shekara hudu - saboda haka a bana ranar 3 ga watan Nuwamba ke nan.
Sauya wannan ranar na hannun 'yan majalisar kasar ne ba shugaban kasa ba.
Saboda haka sai mafi rinjayen 'yan majalisun wakilai da na dattawa sun kada kuri'ar yin haka kafin a iya sauya ranar zaben. Ko shakka babu samun faruwa wannan matakin zai yi wuya ganin cewa tilas dokar ta bi ta hannun majalisar wakilai wadda jam'iyyar Democrat ke da gagarumin rinjaye a cikinta.
Comments
Post a Comment