Buɗe Makarantu: Gwamnan Kwara ya nome ciyawa a sakandare


Buɗe Makarantu: Gwamnan Kwara ya nome ciyawa a
sakandare
Gwamnan Jihar Kwara - da ke tsakiyar Najeriya - AbdulRahman
AbdulRazaq ya jagoranci sauran jami'an gwamnati domin girbe
ciyawa a makarantar sakandare ta Mount Carmel College jiya
Asabar a Ilorin, babban birnin jihar.
A gobe Litinin ne za a koma makarantu a faɗin jihar domin fara
sabuwar shekarar karatu ta 2020/2021.
Gwamnan ya ce ya aikata hakan ne domin ya ƙarfafa gwiwar
mazauna jihar wurin kula da ma'aikatun gwamnati da ke
yankunansu.
Daga cikin waɗanda suka yi masa rakiya akwai jagoran
Majalisar Dokokin Jihar, Magaji Olawoyin da kuma shugaban
kwamitin mahalli, AbdulRazaq Jiddah.
Daga nan sai gwamnan ya zagaya harabar makarantar, wadda
ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan ta shafa.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar ta umarci shugabannin
makarantu da kuma makarantu masu zaman kansu da kar su
karɓi kuɗin zangon karatu na uku daga hannun iyayen yara.
Kwamishinar Ilimi Hajia Fatimah Bisola Ahmed ce ta bayyana
hakan cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin jihar ya fitar,
tana mai cewa sabuwar shekarar karatu za ta fara ne daga
gobe Litinin, 5 ga watan Oktoba.
An dai rufe makarantu a Najeriya yayin da ake tsaka da karatu
tun a watan Maris a yunƙurin mahukunta na daƙile yaɗuwar
annobar cutar korona.

Comments

Popular posts from this blog

Buhari ya ce ba tallafin gwamnati aka wawushe a jihohi ba

KUDUQUFA WAJAN ADU'O'I ~Shugaban Kungiyar ZASDA Yayi Kira

Association with the company and the