An bai wa wasu mutum uku kyautar Nobel kan gano Baƙin Ramin sararin samaniya
An bai wa wasu masana kimiyya kyautar karramawa ta Nobel a fannin kimiyyar Fiziks don ƙoƙarinsu na gano baƙin rami na ''black hole.''
An bayyana sunayen Roger Penrose da Reinhard Genzel da Andrea Ghez waɗanda suka yi nasarar ne a wani taron manema labarai a Stockholm.
Mutanen za su raba kuɗin fam miliyan 864,200 a tsakanin su.
David Haviland, shugaban kwamitin ba da kyaututtukan na fannin fiziks, ya ce kyautar ta bana ta karrama ɗaya daga cikin wasu abubuwa na ban mamaki ne da aka gano a duniya.''
Baƙin rami yankuna ne a sararin samaniya da suke da maganaɗisunsu ke daƙarfi ta yadda ko haske ba zai iya giftawa ta wajensu ba.
Comments
Post a Comment