Ga Jerin Manyan nasarorin DCP Abba Kyari Hamisin 50 daga cikin dari da Hansin 150
ALLAHU AKBAR: Ga Jerin Manyan nasarorin DCP Abba Kyari Hamisin 50 daga cikin dari da Hansin 150 da zan kawo maku.. ~Shine 'dan Sanda Mafi kama 'yan ta'adda a duk tarihin Nageriya... S 1 KAMA: shahararren mai garkuwa da mutanen Najeriya mai suna Chukwudumeme Onwaumadike Aka ‘Evans’ a jihar Legas Wanda aka kama tare da tawagarsa wanda yanzu haka ake kan shari’a. 2 KAMA: wadanda suka kashe tsohon Babban Hafsan Tsaro (CDS) Air Marshal Alex Badeh ‘rtd’ a kan hanyar Keffi-Gitata Kaduna, shima yanzu Shari’a ke tuhumarsu. 3 KAMA: kwamandan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo Umar Abdulmalik tare da mutun Takwas (8) 'yan kungiyar ta'addancinsa shima ana kan bincike. 4 KAMA: 'yan ta'addar Boko Haram ashirin da biyu (22) da suka yi garkuwa da' yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014 sannan kuma su ke da alhakin jerin hare-haren kunar bakin wake/hare-hare da dama da kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Shima shari'ar na kan ...