Posts

Sanata Saidu Umar Kumo ya rasu Sanata Saidu Umar Kumo

Image
Allah Ya yi wa Sanata Saidu Umar Kumo rasuwa da safiyar yau Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020. Tsohon sanatan wanda ya wakilci mazabar Jihar Gombe ta Tsakiya, ya rasu ne a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya. Kafin rasuwarsa, shi ne Garkuwan Gombe. Ya riƙe shugaban kamfe ɗin Alhaji Atiku Abubakar a shiyyar arewa maso gabas a zaɓen shugaban ƙasa na 2019. Sai dai Sanata Kumo ya koma jam'iyyar APC mai mulki a watan Janairun 2019 kafin a shiga zaɓen da Muhammadu Buhari ya lashe a watan Fabarairu. An zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa a shekarar 1999 zuwa 2003 kafin daga baya ya yi takarar gwamnan Gombe a 2011, inda ya sha kaye a hannun Ibrahim Hassan Dankwambo. Za a yi jana'izarsa a Masallacin Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

GWAMNATI TA DAKATAR DA YIN REGISTER LAYUKA

Image
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ce ta ba da umarnin ga kamfanonin sadarwa har sai ta gama tantance layukan wayan da ake amfani da su a kasar. Ta ce Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sa a tantance layukan wayan da ba a yi wa cikakken rajista yadda ya kamata ba. Sanarwa da Daraktan yada labaran NCC, Ikechukwu Adinde, ya fitar ta ce yin hakan ya zama dole kuma duk kamfanin da ya saba, to zai yaba wa aya zaki, da zai ga soke rajistarsa.
Image
YAKI NUNA TAUSAYIN SA - 👉AISHA YESUFU.  ZABARMARI | Akwai matukar kona rai, a ce 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram su fito su yi magana akan kisan gillar da suka yiwa al'umma anma Buhari yaki" - Inji Aisha Yesufu.

ZABABBEN SHUGABAN KASAR AMURKA YA KARYE A KAFA

Image
BABBAR MAGANA: Zababben Shugaban Amirka Joe Biden ya karye a kafarsa. Biden mai shekaru 78 ya karye a yayinda yake wasa da karnukansa a karshen mako. Likitan Biden ya ce shugaban na Amirka mai jiran-gado na bukatar watakila sai yayi amfani da takalmin likita kuma zai kwashe makonni kafin ya kammala wannan jinya. Karyewar kafar ta zababben shugaban na zuwa ne 'yan makonni kalilan kafin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasar ta Amirka a watan Janairu mai zuwa.

The Colonialism Of The British Empire is Abate the Hausa Land by Muhammad Auwal Ibrahim Zauma

Image
the colonialism of the British Empire is Abate the Hausa Land with Insecurity, Recession and Destitution of poverty everything past before the the British colonialism came to Nigeria in 1884 we In Northern region (Hausa Fulani ) Have our own policy of Evoking Security in our region apart of Farming in 1911, the Hausa of northern Nigeria became major producers of groundnuts. They surprised the British, who had expected the Hausa to turn to cotton production However, the Hausa had sufficient agricultural expertise apart Marketing we are not left behind By the 12th century AD the Hausa were becoming one of Africa's major trading powers its Scandal and Frustrated the moment we are today in Hausa land we out our mind our senses go far from us we thought democracy can solve all our problems

ZANGA ZANGAR KIN JININ FARANSA

Image
You jumu'a zanga zangar kin jinin Faransa na cigaba da gudana a fadin Kasar. 

An raunata wani mai gadi a ofishin jakadancin Faransa a Saudiyya

Image
An kama wani mutum a birnin Jidda na kasar Saudiyya da ake zargi da raunata wani maigadi a ofishin jakadancin Faransa da ke birnin, ta hanyar daba masa wuka. Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani a kan abin da ya haddasa harin. Sai dai harin ya biyo bayan zaman dar-dar din da ake yi a gabas-ta-tsakiya, sakamakon matsayin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya dauka na kare zanen batancin nan da aka yi na aibanta Annabi Muhammadu. Tuni dai Ofishin ofishin jakadancin Faransar ya gargadin Faransawa mazauna Saudiyya da su dinga taka-tsantsan.