Posts

Showing posts from December, 2020

Sanata Saidu Umar Kumo ya rasu Sanata Saidu Umar Kumo

Image
Allah Ya yi wa Sanata Saidu Umar Kumo rasuwa da safiyar yau Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020. Tsohon sanatan wanda ya wakilci mazabar Jihar Gombe ta Tsakiya, ya rasu ne a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya. Kafin rasuwarsa, shi ne Garkuwan Gombe. Ya riƙe shugaban kamfe ɗin Alhaji Atiku Abubakar a shiyyar arewa maso gabas a zaɓen shugaban ƙasa na 2019. Sai dai Sanata Kumo ya koma jam'iyyar APC mai mulki a watan Janairun 2019 kafin a shiga zaɓen da Muhammadu Buhari ya lashe a watan Fabarairu. An zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa a shekarar 1999 zuwa 2003 kafin daga baya ya yi takarar gwamnan Gombe a 2011, inda ya sha kaye a hannun Ibrahim Hassan Dankwambo. Za a yi jana'izarsa a Masallacin Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

GWAMNATI TA DAKATAR DA YIN REGISTER LAYUKA

Image
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ce ta ba da umarnin ga kamfanonin sadarwa har sai ta gama tantance layukan wayan da ake amfani da su a kasar. Ta ce Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sa a tantance layukan wayan da ba a yi wa cikakken rajista yadda ya kamata ba. Sanarwa da Daraktan yada labaran NCC, Ikechukwu Adinde, ya fitar ta ce yin hakan ya zama dole kuma duk kamfanin da ya saba, to zai yaba wa aya zaki, da zai ga soke rajistarsa.
Image
YAKI NUNA TAUSAYIN SA - 👉AISHA YESUFU.  ZABARMARI | Akwai matukar kona rai, a ce 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram su fito su yi magana akan kisan gillar da suka yiwa al'umma anma Buhari yaki" - Inji Aisha Yesufu.